Fitaccen jarumin barkwanci nan a masana'antar fina-finai ta Kannywood, Mustapha Badamasi, wanda a ka fi sa ni da Mustapha Naburaska, ya bayyana cewar, shi farkon shigowar sa cikin masana'antar fina-finan Kannywood ba ya shigo ba ne da niyyar ya zama jarumi ba a cikin masana'antar, sai kuma ga shi ya samu kan sa a matsayin jarumi. Northflix na ruwaito.

Mustapha Naburaska, ya fadi haka ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da yadda ya samu kan sa a cikin masana'antar, ya na mai cewa, "

"Ina ganin za a iya cewa a lokacin da na fara harkar nan ta fim, ni ban shigo da niyyar na zama jarumi ba, na zo ne na zama ko dai marubuci, ko furodusa ko dai wani da ya ke bayar da gudummawa ta wata hanyar da ba ma sai an haska ni ba. To dai bukata ta shi ne, mu hadu mu magance matsalolin da su ke damun matasa maza da mata. Wannan ya ja hankali na ya sa na shigo masana'antar, domin na bayar da tawa gudummawa a cikin ta. Amma cikin ikon Allah sai gashi na samu kai na a matsayin jarumi, kuma dan wasan barkwanci, wanda a yanzu cikin ikon Allah, ina daya daga cikin wadanda za a kalla a ce ina daga cikin 'yan wasan barkwanci". Inji Naburaska.

Mun tambaye shi dangane da dadewar sa a cikin masana'antar, ko ya kai shekaru nawa a cikin ta?

"To ina ganin yanzu na kai shekaru 19 a cikin masana'antar, duk da na yi wasu ayyuka da dama a cikin masana'antar, amma dai an fi sa ni na a matsayin dan wasan barkwanci, domin shi na fi kwarewa a kai, kuma jama'a da shi a ka fi sanina, kuma babban kamfanin iyayen gida na shi ne na su, Sani Danja da Yakubu Muhammad, su ne iyayen gida na kuma sun ba ni gudummawa sosai, kuma har gobe ina yin alfahari da su, domin ba ni da iyayen gidan da su ka kai su a cikin harkar fim duk da cewar daga baya na koma bangaren Rabilu Musa Dan Ibro, wanda daga nan na zama dan wasan barkwanci, domin haka a yanzu dai ba bu abun da zan ce dangane da harkar fim dai sai godiya ga Allah, domin ita ce ta daga ni duniya ta sanni ko da ina yin harkar siyasa, to ita ma ta samu ne ta dalilin fim din, domin haka ina kira ga mutane da su rinka rike sana'ar su da muhimmanci domin sana'ar mutum mutunci sa". A cewar Mustapha Naburaska.

Sai dai kuma ya yi kira ga masoyan sa na harkar fim da cewar, ya na tare da su dari bisa dari. Haka ma masoyan sa na siyasa su ma ya na tare da su, kuma dukkan su ya na yi musu fatan alheri.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top