Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta koka kan yawaitar matsalar cin zarafin mata, tana mai cewa, ta tattara alkaluma 606 na fyade da aka yi kananan yara mata a bara kadai. Jaridar Labari24 na wallafa

Shugaban Hukumar ta Hisbah, Dakta Adamu Bello Kasarawa ne ya bayyana haka, inda ya ce, matsalar ta zarta wadda aka gani a shekarar 2018, lokacin da aka tattara alkaluma 296 na fyaden.

A cikin watan Janairun bana, Hukumar ta samu korafin fyade har sau 31, abin da ke nuna kazancewar matsalar.

Akasarin matan da ake yi wa fyaden ba su wuce shekara 5 zuwa 16 ba a cewar shugaban na Hisbah.

Daga cikin masu aikata fyaden har da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da limamai da attajiran ‘yan kasuwa maza da mata kamar yadda Dakta Kasarawa ya yi karin bayani.

Jami’in ya bukaci gwamnatin Sokoto da ta tallafa wa Hukumar ta Hisbah da kayan aiki kamar motoci domin yakar matsalar fyade da sauran ayyukan assha a jihar.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top