Wannan mummunan abu daya faru da Maryam Booth ya zama darasi da izina musamman ga iyaye mata, ina tuna takaddamar data faru  tsakanin Hukumar tace fina-finai da su Maryam Booth da mahaifiyarta da ma Kannywood shekaru goma sha baya, a lokacin Dr Malam Abubakar Rabo Abdulkarim ke shugabancin Hukumar ta tace fina-finai.

Mahafiyar Maryam booth ta kawo 'yarta masana'antar shirya fina-finai  tana karamar yarinya, ina tunanin a lokacin bata wuce shekara goma sha hudu ba, kuma an fara saka ta a fina-finai ana bata matsayin da zata iya, a lokacin ne kuma Shugaban Hukumar tace fina-finai Dr Malam Rabo ya daura damarar kawo gyara a cikin masana'antar ta Kannywood ta hanyar tabbatar da doka da oda domin sauke amanar da gwamnatin Kano ta dora masa.

An fara samun sabanin tsakanin Hukumar tace fina-finai da Maryam Booth a lokacin da hukumar ta shimfida wasu dokoki da ka'idoji wanda dole sai mutum ya cika su sannan za'a sahale masa fitowa cikin fina-finai, sai aka sami akasai ita wannan yarinya ta gaza cika wadan nan sharuda da ka'idoji domin a lokacin bata cika shekara sha takwas ba kamar yadda doka ta tanada, bugu da kari tunda ta kammala primary ta watsar da karatu, wanda hakan yasa Shugaban Hukumar na wancan lokaci yayi shakulatin bangaro akan yi mata register, wanda har takai uwarta ta sako ta a gaba sun nemi ganin Malam Rabo inda ta nemi alfarma akan ayi wa yarta register amma Malam Rabo be amince ba, inda ya baiwa uwarta ta shawarar karatu ne yafi cancanta da ita da kaninta ba harkar wasan film ba, domin idan har yayi musu register ya karya dokar hukuma, karya dokar hukuma kuwa cin amanar gwamnati ne, a lokacin har Malam Rabo yasha alwashin taimakawa yaran ta hanyar basu tallafin karatun gwamnati domin su inganta rayuwarsu, daga nan ne uwar tayi godiya ta tafi.

Hallau dai uwar tayi amfani da abokan Malam Rabo da wadanda yake mutuntawa ta hanyar rokonsu kan su lallame shi yayi wa 'ya'yanta register domin a dinga saka su cikin fina-finai amma hakarta bai cimma ruwa ba.

Daga nan ne kuma suka fara maganganu marasa dadi kan cewa hukumar tace fina-finai ta zalunce su ta tauye musu hakki, har ita Zainab Booth din suka hadu da Adam A Zango da Rabilu Musa Ibro da 'ya'yanta Maryam Booth da Amude Booth suka shirya film na batanci wa Malam Rabo sunan film film shine IBRO RABON WAHALA inda suka ci mutuncin rabo, bayan nan Adam A Zango da Ibro da ita wannan yarinya sun shirya fina-finai da wakoki suna cin mutuncin Rabo, laifin Malam Rabo a wajensu shine bin doka da oda.

Hakika Allah ne kadai yasan damuwa da bakin cikin da Videon tsiraicin Maryam Booth ya sanya mahafiyarta, dama hausawa sunyi gaskiya da suka ce" tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka", yau da ace mahaifiyar wadan nan yara tabi maganar Malam Rabo ta hanyar basu tarbiya su zamanto mutane da abun da ya faru watakila bai faru ba.

Masu magana dai kance" Ganin buzu a masallaci ya ishi Tunkiya daukan darasi".

I.A.I

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top