TY Sha’aban ya tabbatar da hakan ne yayin wata tattaunawa wakiliyar mu, inda ya ce shi ya na cikin masana’antar Northflix Na wallafa

A kwanakin baya akwai wani fim da ku ka shirya mai suna Tauraron Boye, wanda a cikin wannan fim din ka saka danka Free Boy a ciki, sannan fim din ya jawo daukacin hankalin jama’a musamman a shafukan sada zumunta sakamakon sunan shi da ya yi kamanceceniya da wani fim na Amir Khan. Shin labarin ya na da nasaba da wancan labarin ko kuwa wani ne daban?

A jawabin say a fara da cewar “Kinsan a masana’antar shirya fina-finai ta duniya, za ki ga cewar suna yakan zo daya, amma abun da labarin ya kunsa ya na bambanta, to a wannan ma haka abun yake suna ne wannan na Secrete Superstar, wancan ma haka suna daya, sunan shi ne kamanceceniyar amma kowane labarin ya sha banban”.

Bayan harkar wake-waken da danka Free bo ya ke yi na ga yanzu ka sa shi a fim wannan ya na nufin danka ya yi fim kenan?

“Eh to, gaskiya ni ban  ma yi zaton yaron ya na da baiwa ta waka ko shawa’a na harkar fim ba, sai daga bayan nan, abun da na saka a gaba shi ne ganin na bawa yarona da iyalina ilimin da ya kamata da tarbiya bisa tsarin addinin musulunci da zamantakewar al’umma, amma Allah da ikonsa da ya taso sai na yi kokarin na gwadashi a fim, domin ya yi fim da yawa kafin wannan Secret Superstar, sai da ya fara yin fina-finai kafin ya yi waka, kuma wakar sai daga baya ya zo ya same ni ya ce, ya iya waka kuma ya na da sha’awar yin wakar, wannan ya sa na bashi dama na gwadashi kuma na ga ya na da basirar yin wakar kamar yadda ya fada, amma fim din ma ya fara yi kafin waka”.

Ya dade kenan ya na fim ko kuwa kwanan nan ya fara?

“Eh to, fim din sa na farko shi ne wanda a ka yi a jihar Zamfara da dadewa lokacin bai fi shekara shida ba, shi ne Malika na Ali Nuhu da Maryam Malika, daga nan sai komai Nisan dare da sauransu”.

Amma kai ma a kankin kanka zan iya cewa an kwana biyu ba a jin duriyar ka a fina-finai, sai kwanakin nan wannan ya na nufin ka dawo harkar fim kenan?

“Ai dama ban tafi ko Ina ba, ina nan a harkar fim, domin haka kin ga ai ba a ce na tafi na dawo ba, shi harkar mu ta Multimedia ta na da bangarori da dama, mutum zai iya zama furodusa, darakta ko dai wani abun daban wanda ba za a gan shi ba, sannan bayan wannan akwai hanyoyi da bangarori na gidajen talabijin da rediyo da na ke tabawa da bangaren tallace-tallace, duk wadannan sune abun da suke sakani yau ina can gobe ina can, na zama koda yaushe a cikin aiki har ta sa a ke ganin kamar na tafi ne amma Ina nan gaskiya ba bu inda naje a masana’antar. Misali yanzu alqiblata bayan na gama daukar tauraron boye shine bidiyon album na yaro na da na ke dauka, kuma muna sa ran wannan shekarar za mu yi kaddamar da shi, jama’a su gani da idonsu irin basirar da yake da ita”. Inji TY Sha’aban.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top