Matasa da dama suna kukan rashin aikin yi da talauci, amma abunda zai baka mamaki irin yadda suke bata lokacinsu da kuma kashe kudadensu akan shiga kafafen yada labaru na zamani ba tare da sun amfani kawunansu ba.
Duk da yake wandanda suka kirkiro wadannan kafafen manufansu bai wuce yadda zasu kulla zumunci ko halaka tsakanin mutane ba. Amma tuni masu dabara da hangen nesa sun gano hanyoyin da ake iya samun makudan kudi dasu.
Maimakon bata lokacinka kana yiwa 'yan siyasa bambamdanci da fushi da fushinsu. Ko kuma bata lokaci kana hira da 'yan mata ko kana daukan hotunan kana posting, ina ganin idan zaka yi amfani da wadannan hanyoyin guda biyar a social media dinka nan da wasu lokuta zaka huce takaici da talauci ya jefaka.
Abun sha'awa ga neman kudi a shafukanmu na social media kowa na iya yi, mata sunma fi samun dama musamman mantan dake zaune basu da aiyukan yi. Haka kuma koda mutum ma'aikaci ne zai iya neman kudi a shafinsa.
Na aha yin bayanin yawan mabiyanka a shafukanka, yawan jarinka idan ka iya amfani dasu yadda ya kamata. Akasarin hutunan da nake sawa a storyline dinna a Facebook biyana akeyi duk bayan awanni 24, Kuma da dalar amurka. Masu aibata hutunan da masu son hutunan dukkansu ina samun kudi a dalilinsu
Ba cewa nayi mu daina yiwa 'yan siyasa maula ko bata lokacinmu akansu a social media ba, kana iya hada biyu idan zaka iya kamar yadda nake yi. Amma dai idan lokaci yayi kai da kanka zaka rage ko zaka daina muddin ka himmatu da samun kudin shiga.
Ga wasu hanyoyin samun kudin da shafukanmu na social media Lamar haka.
1: Bincike- akwai kamfanoni da dama da suke neman wadanda zasu masu bincike akan wani lamari ko wanj abu. Irin wwdannan kamfanonin suna neman mutanen da suke da mabiya a shafukansu domin gudanar da wandannan aiyukan. Wasu lokatan ma harma da wadanda basu da mabiya sosai.
Misali idan wani kamfani yana son ya shigo da sabon samfurin audugar kunzugun mata, ko kuma yana son ya kafa kamfanin a Nijeriya zai bukaci a binciko masa mata nawa ne suke amfani da kuzugun, kuma nawa suke iya sayansa, kuma wani farashi ya kamata a saya a kasuwa. Kuma wani yankin kasar ne sukafi amfani dashi. Da wannan binciken ne za a yi amfani domin gudanar da kasuwanci. Irin wadannan kamfanin ko yanzu suna matukar neman wadanda zasu musu research domin biyansu. Misalin irin wadannan kamfanonin ga https://ift.tt/2u4d0NL da zaku iya tuntuba.
2: Yin Talla- Da akwai kamfanonin da suke bukatar yayata kayan da suke kirewa. Abunda kawai suke so kayi shine ka musu tallan kayansu a shafinka, tare da bada adireshinsu ga mabukatan kayansu. Zasu rika biyanka ne yadda kuka amincewa juna.
Wannan shima hanyace mafi sauki wajen samun kudi ta shafinka na social media. Kuma akwai kamfanoni da damar dake bukatar hakan. Kamfanoni irinsu
NOTABLE PROJECT suna baiwa masu bukata aiyuka da tallace-tallace a social media.
3: Dilanci- Kana iya zama dilali da shafinka na social media idan ka kawo mai bukata ko ka sayar ka samu kamishion dinka hankali kwance.
Shafukanka na Facebook, whatsappp da sauransu na iya zama wajen da zaka tallata wani abu da aka baka dillancinsa ta hanyar saka hotunansu domin mabiyanka su gani.
Kana iya tuntunban kamfanoni domin tallata musu kayamsu. Ko shagunan masu sayarda kayan sawa harma da masu sayar da da gidaje, bada haya da motoci.
Yanzu haka basai ka bari zuwa gobe ba kana iya somawa ta hanyar tuntubar mutane ko kamfanonin da kake son yin wanna huldar dasu.
4: Saka Bidiyo ko Murya- A wannan bangaren kana bukatar kirkiro naka shafin YouTube ne dashi ne zaka yi amfani domin samun kudi.
Idan ka samu shafinka na YouTube kan iya kirkiro wani shiri da zaka rika daukarsa ta video ko kuma Maurya domin sakawa a shafinka duk wanda ya saurara ko ya kalla zai biya.
Misali ka kirkiron wani shirin tonon silili, gulma ko abunda mamaki da ba safe ake jinsu ko ganinsu ba. Kana iya zuwa ka hira da wani wanda ya shahara a wani bangare na rayuwa. Kana iya zuwa ka samu labarin wanda kafafen yada labarai basudashi ka saka.
Da zaran ka saka sai kuma ka kowa shafukanka ka tallatan shirin naka tare da bada adereshin shafinka domin masu kallon su kalla kuma suyi subscribing.
Tuni mutane da dama suka zama masu kudi ta wannan hanyar.
5: Yin Tall an Bukukuwa Ko Tarurunka- Mutane da kamfanoni da dama suna kashe kudi masu dunbin yawa wajen son tallata ko gayyatar mutane ko su sanar dasu wani buki ko taro ko ma wani sabon abu da suka yi.
Kana iya ziyartan irin wadannan wuraren domin neman su baka aikin tallatamusu hidimominsu da sukeson gudanarwa.
Wadannan sune kadan daga cikin hanyoyin da zaka samu kudi cikin sauki ta shafinka na social media da ka maidashi dandalin bata lokaci na yin gulma da tsaigumi, bambadanci da fushi da fushin wasu.
Ga masu kwarewa akan koyarwa ko illimin wani abu, suna iya samun aikin koyarwa online suma. Akwai kamfanoni da dama da suke baiwa dalibai da malamai aikin karantarwa online ko kuma yi musu wani assessment da dalibansu, kuma kudi suke biya masu tsoka. Guda daga cikin wannan kamfanin shine Acadamicia ga address dinsu https://ift.tt/2rGzQdw. Idan kayi rigista dasu wanda kyauta ne. Akwai aiyuka da daman gaske da malamai da daibai a zube, zaka duba wanda zaka iya da kudin da za abiyaka da kuma lokacin da ake bukatar ka kammala aikn. Wallahi kana gaba aikin kamar yadda suka nema kayi kana ganin alart kuma a dala.
Baka bukatan jari, da yawuce wayanka da datarka. Baka bukatar shago ko rumfa, kana kwance a kan gadonka zaka iya gudanar da wannan harkar.
Kawai abubun bukata kayi kokari jawo mabiya dayawa domin tanan ne duk masu baka aiki zasuyi la'akari. Idan kana da mabiya da yawa zaka a biyaka da yawa.
Allah sa a soma a sa'a
© Sirrinrikemiji
Post a Comment