*💖🥀Abu ya'ala ya riwaito a musnad (1868)! Wata mata tazo wajen annabi saw tace! Ya manzon Allah! Mijina baya kusantata! ka raba aurena dashi! Sai mijinta ya bijiro gurin annabi saw ya kirasa yace! Me yasa baka kusantar matarka? Yace Wallahi ko jiya na kusanceta! Kawai sai ta fashe da kuka tace! Wallahi karya yake yi! Kuma yana cikin mafi kiyayyar halittar Allah aguna🤣🤣 Sai annabi saw yayi murmushi yace! Ya Allah ka hada hankulansu...*

*💖🥀Bayan dan lokaci! matar tazo wajen annabi saw tace! Wallahi ba wanda nafi so kamar mijina! bayan kai..*

*👇🏼DARASI A WANNAN KISSAR👇🏼*

*💖🥀1)) Takatsatsan wajen shedar mata akan mazajensu! Domin mata da yawansu in basa son mutum kowane sharri da kage suna iya lafta masa, ko abunda baki-baki ne, su mayar dashi baki kirin-kirin! Haka ta gefe daya! Akwai buqatar takatsantsan ga itama shedar miji akan matarsa...*

*💖🥀2)) Raunin shedar mata, shi yasa ko a sharia shedar macce matsayin rabin shedar namiji take..*

*💖🥀3)) Idan zakayi qiyayya da mutum to ka taqaita a qiyayyarka da shi, mai yiyuwa gobe zai mamaye zuciyarka...*

*💖🥀4)) Takatsantsan da kukan mata! gudun kada ya zama kukan ka cuci mutum kuma ka masa kuka. Shi yasa zamu ga annabi saw dariya ma yayi ga kukan matar...*

*💖🥀5)) Sasantawa a tsakanin maaurata, da kyakyawar addu'a ga zamantakewarsu...*

*💖🥀6- Mu'ujizar annabi saw*


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top