Bikin murnar zagayowar sabuwar shekarar alama ce ta shiga sabuwar shekarar miladiyya kuma mutane da yawa na taya juna murnar shiga wannan sabuwar shekarar.. Malamai da yawa kan bayyana cewa babu kyau kuma addinin musulunci bai amince da a yi wa Kiristoci murnar zagayowar sabuwa shekara ba.
Madogara: Legithausa

Malamai dayawa na addinin Islama kan bayyana cewa babu kyau wannan gaishe-gaishen da taya murnar sabuwar shekara. Sanannen abu ne cewa akwai bukukuwa uku a musulunci, sun hada da Juma'a, Sallah karama da kuma babbar Sallah.

Baya ga wadannan bukukuwan, babu wata murna da aka amince a taya 'yan uwa da abokan arziki.

Musulmai basu bikin murnar sabuwar shekarar Hijirah, shekarar musulunci. Farawa da amsa gaishe-gaishen shekarar miladiyya kuwa tamkar riko da hakan ne.



Ya kamata musulmai su dinga alfahari da addinin su da koyarwarsa. Idan har amma aka yi maka barka da sabuwar shekara, zaka iya mayar da martani da kalamai kamar haka "Ina fatan ka mori hutunka/ki".

Zamu iya cin abincin Kiristoci saboda su ma 'yan uwanmu ne amma ba zamu iya shiga bukukuwan taya murna irin nasu ba kamar Kirsimeti ko sabuwar shekara.

Kamar yadda Ibn Al-Qayyum ya bayyana a litttafinsa mai suna Ahl-al-Dhummanis ya ce: Taya wadanda ba musulmai murna ba a lokutan shagalinsu Haram ne kamar yadda aka yi ittifaki a kai.

Kirsimati da sabuwar shekara duk ba bukukuwan musulmai bane.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top