Northflix na ruwaito.
Tun kafin lokacin dai yan fim din Kannywood su ka cika shafukan su na sada zumunta da tallata taron tare da rungumar sa a matsayin taron da su ke da ruwa da tsaki a cikin sa, don haka su ka tashi tsaye wajen tallata bikin.
Sai dai a lokacin da a ka shiga taron wasu 'yan fim din su ka fara korafin cewar taron ba a shirya domin su ba, don haka ne ma wasu su ka fice daga wajen, ya yin da wasu kuma da su ka zauna, sai su ka fahimci kan su a matsayin yan kallo, domin kuwa ko da wajen zama na musamman ba a tanadar wa yan fim din Hausa ba. A Yadda wani wanda bai yadda a ambaci sunansa ba ya bayyana
kuma ba a basu wata damar da zasu gabatar da komai a wajen ba, sai dai kawai su zuba ido su na Kallo tare da sauraro. Sannan abin da ya fi jefa tambaya zukatan yan Kannywood a kan shi BON AWARD din shi ne ko akwai finafinan Kannywood a finafinan da a ka shigar a gasar? Saboda babu fim din Hausa ko daya a zababbun finafinan da a ka gabatar, duk kuwa da cewar a Kano cibiyar finafinan Hausa a ka gudanar da taron.
Wannan ce ta sa tun a cikin dakin taron wakilin mu ya tambayi Darakta Yasee Auwal dangane da rashin finafinan Hausa a cikin gasar, in da ya shaida mana cewa “Babu wani abu da mu ka sani a cikin wannan Award din, an dai gayyaci yan fim ne su zo wajen taron, amma maganar shigar da finafinan mu, ba a sanar da mu ba. kuma gasa idan za ka shiga ana sanar da kai ne lokacin da za a fara shigar da fim da lokacin da za a rufe amma mu dai an ce za a yi taro ne a Kano kuma aka gayyace mu, ko da ya ke na ga an kafa kwamitin taron a cikin yan fim din mu su na aiki a ciki.”
Ya kara da cewa “Amma dai idan ka duba finafinan da su ke cikin gasar za ka ga ba su kai namu da mu ke yi ba, don haka su ma ba wasu fitattun finafinai ba ne ko a can Nollywood din don haka za ka ga jaruman fim din ma da su ka zo ba wasu fitattu ba ne".
Jarumi T Y Shaba shi ma ya yi korafi tare da sukar yadda a ka gudanar da taron a shafin sa na Instagram inda ya ke cewa “Abin takaici ne a zo Kano a yi taron amm yan Kannywood babu wata dama da a ka ba su, domin babu mawakan Kannywood ko daya da a ka saka wakar sa a wajen duk da kuwa da kudin jihar Kano a ka shirya taron amma a gaban Gwamna a ka mayar da mutanen Kano baya, kuma wasu abubuwan ma da a ka rinka yi a wajen cin mutunci Kano ne da al'adun Kano, don haka abin kunya ne a nunawa Duniya cewa a Kano a ka gudanar da wannan taron. Akwai abubuwa masu yawa da a ka yi a taron wanda ba za su fadu ba, amma dai mu abin da mu ke gani shi ne an ci mutuncin mu a wannan taron.” A cewar TY Shaba
Sai dai dangane da korafin da wasu daga cikin ‘yan fim din da su ke yi, mun nemi jin ta bakin shugaban Hukumar tace finafinai da Dab’i ta jihar Kano Alh. Isma’il Muhammad Na’abba wanda a ka fi sani da Afakallah wanda su ne shugabanin taron ta bangaren Gwamnati kan yadda a ka yi taron da yan fim su kecewa bai wakilci Kano ba, in da ya ke cewa "taron ya wakilci kowa har da mutanen Kano. Amma abin da ya kamata mutane su sani shi ne taron sunan sa Best of Nollywood ba Kannywood ba. kuma ba yanzu a ka fara shi ba, wannan shi ne Karo na 11, an shi a garuruwa da dama a kasar nan kuma an saka yan fim din Hausa a ciki wadanda su ka samu award kamar irin su Rahama Hassan, Fati Ladan, Nafisa Abdullahi, da sauran su.
To wannan taron da aka zo a ka yi a Kano daman nema su ke yi Gwantocin jihohi su ba su tallafi domin su gudanar da taron su, kuma su na neman tallafi daga kamfaninnika ma. Domin haka su ka zo su ka nema, kuma Gwamnatin Kano ta ga za ta iya yi, saboda bunkasa harkar kasuwanci a jihar, shi ya sa a ka zo a ka yi. Abin da ya kamata yan Kannywood su fahimta, yanzu duniya dunkulewa a ke yi sai a yi nasara. Amma ka duba duk AWARD din da a ke yi a Kannywood, kowa tasa ya ke yi, kowa y
©HausaLoaded
Post a Comment