Ya biya sadakin ta. 
Ya rike ta amana cikin girma da arziki, da kyautatawa.

Kar ya cutar da ita kuma kar ya bari yana sane a cutar da ita ko ya buɗe wata hanyar da za'a cutar da ita ya zamo garkuwa gwargwado iko a gare ta.

kada ya jinkirta wani bukatan ta ko hakkin ta, ba tare da wani kwakkwaran dalili ba yaji tsoron ALLAH. 

Ya dunga wasa da dariya da ita a gabadaya rayuwar su na aure, kamar yadda Annabi muhammad (S.A.W) yake yida matan sa, hakan na sabunta soyayya madauwamiya a zuciyoyin su da rashin gajiya da juna da marmarin juna.

Yayi hira da ita kamar yadda Annabi (S.A.W) yake zama da matayen sa, suyi hira kuma ya saurare su. 

Ya karantar da ita ilmi na addini kuma ya kara karfafa mata gwuiwa akai, ko ya kaita ingantacciyar makarantar sunnah ta samu ilmi ya dunga tunatar da ita hakkin ALLAH a kanta taji tsoron ALLAH, da kuma gyara mu'amulolin ta. 

Ya dunga lura da Kuskuren ta yana mata gyara cikin so da qauna cikin rarrashi har ta gane, ya kuma dunga yabon ta in tayi abu daidai na kyautata wa idan da hali yayi mata kyauta ma akai iya karfin sa. 

In tayi Kuskure da ya sabawa addini ya nuna mata tayi Kuskure, kuma ya taya ta da addu'a sa'annan yayi mata nasiha. 

Kar ya zamo mai cutar da ita ta hanyar duka ko ya mari ta ko zagi.

Kar ya zamo mara sirri yana tona mata asiri ya zamo duk abunda sukayi a rayuwar auren su yaje yana fadawa mutane a waje, wannan haramun ne ba siffa ce ta miji na gari ba.

Yabi duk sare saren musulunci yadda musulunci ya nuna a kyautata wa mace ya kuma dunga sauke mata hakkin ta gwargwadon iko. 

Ya zamo taimaka mata ko Yan uwanta a duk Lokacin da take bukatar taimako gwargwadon iko, kuma ya rike ta amana. 

Ya zamo mai girmama iyayen ta, ya kuma nuna mata kulawa. 

Ya siya mata duk wani kaya mai kyau na sutura ko na gyaran jiki ko kwalliya wanda za ta dunga masa kwalliya a cikin gida. 

Ya zamo Mai kishin ta, domin ma ai wajibi ne ya zamo miji yana kishin matarsa da nuna Soyayya a gare ta. 

Ya zamo mai ciyar da ita halal, yafita ya nemo musu abunda zasu ci halal kuma ya tsare musu mutuncin su. 

Idan yayi mata laifi ya zamo Mai neman ta gafarta masa. 

Ya dunga sanya mata farin ciki, har ya zamo fara jin ba wanda ya fita dacen miji nagari. 

Ya dunga tayar da ita suna wasu ayyukan ibada tare, inda sarari suci abinci tare suyi hira suyi dariya tamkar mata da miji tamkar saurayi da Budurwar sa tamkar yaya da qanwa su zama tamkar ɗaliba da malamin ta. 

Ya zamo Mai tausaya mata da nuna mata lallai ita macece kyakkyawa yar amana mai mutunci yar gidan mutunci mai cikakkiyar ni'ima kuma sarauniya abun girmama wa. 

✍Rashededah Bintu Abeebakar (daughter of Islam)


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top