Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara

- Hakan ya biyo bayan tsayawar da gwamnan yayi wajen ganin ya wanzar da zaman lafiya a jihar

- Buhari yace Matawalle ya nuna kishi sosai akan jiharsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jadadda cewa ya zama dole a fito fili a rika jinjina wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle saboda jajircewar da yayi wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan yankin Arewa da suka ziyarce shi a fadar shugaban kasa karkashin jagorancin sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar III a jiya Juma’a, 23 ga watan Agusta.

Shugaban kasar yace: “Ina kira ga gwamnatocin jihohin kasarnan da su yi koyi da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan yadda ya maida hankali wajen ganin zaman lafiya ya tabbata a jihar Zamfara da kuma irin matakan da yake bi domin samun nasara a kai.




Matawwalle ya nuna kishi matuka da son zaman lafiya a jihar ta hanyar hada kan mutanen jihar.”

©HausaLoaded

Post a Comment

Emoticon
:) :)) ;(( :-) =)) ;( ;-( :d :-d @-) :p :o :>) (o) [-( :-? (p) :-s (m) 8-) :-t :-b b-( :-# =p~ $-) (b) (f) x-) (k) (h) (c) cheer
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.

 
Top