Shahrarren malamin addinin kuma kwararren
farfesan sadarwan ya karytata wannan labari ne da safiyar Asabar, 24 ga watan Agusta a shafinsa na Tuwita. Ya ce gaba daya bai yi magana a kan hakan ba, innama sakataren ma'aikatar ne yayi ishara akan hakan.
Ya ce ma'aikatar zata gabatarwa Najeriya takardan ayyukan da za ta gudanar domin su karanta kuma su fahimci inda suka dosa.
Yace: "Labarin da jaridar The Nation ta wallafa ba gaskiya bane kuma yaudara ne. Ban fadi hakan ba, saboda haka ayi watsi da shi. Abinda nike yanzu shine fahimtar ma'aikatar.
Baya ga haka, zamu gabatarwa yan Najeriya abubuwan da mukayi nufin yi domin su karanta. Sakataren din-din-din ne yayi magana akan al'amarin a matsayin shawara."
Mun kawo rahoton cewa Ministan sadarwa, Dr Isa Ali Pantami ya shiga sabuwar ofishinsa domin fara aiki.
Ministan yayi kira ga ma’aikatansa da cewa su zage dantse domin samu damar cika aiki da Shugaba Muhammadu Buhari ya daura a kansu.
©HausaLoaded
Post a Comment