Cikin wata rubutacciyar takarda da ta fito daga fadar mai martaba Bahindin Bugudo na karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sambo Kaliel, an shimfida sabbin dokoki ga al'ummar gundumar kan sha'anin aure da zanen suna.

Kamar yadda rubutun takardar ya bayyana, "mu mutanen kasar Bahindin Bagudo, mun zauna mun shata dokokin da suka shafi sha'anin aure da zanen suna domin saukakawa jama'armu wahalhalu bisa ga sunnar Annabi Muhammad (S.A.W)."

Dokokin sune kamar haka:

1. Shiga Gida: Kwandon Goro daya da naira dubu biyar (N5,000).

2. Hira: Mai bidar yarinya aure ba zai yi hira da ita da daddare ba sai dai da rana.

3. Kwaryar Sallah, Kayan Sallah da Kayan Shayi: Doka ta soke wannan abubuwa da ake yi.

4. Sadaki: Sadaki kada ya yi kasa da rubu'in dinari akalla, amma ba ya da iyaka.

5. D.J: Doka ta hana yin D.J wurin bikin aure da zanen suna.

6. Kida: Doka ta soke yin kidi da roko wajen bikin aure da zanen suna.

7. Gara: Doka ta hana yin gara, amma ana raka amaryar da buhu hudu na abinci da kayan miya.

8. Yinin Biki: Doka ta yarda Mata su je wurin yinin biki, amma an hana kidi da D.J waejn biki.

9. Wankin Amarya: Doka ta hana wankin amarya a waje, sai dai cikin gidan mahaifinta.

10. Rali: Doka ta soke yin Rali.

11. Picknic: Doka ta hana yin Picknic.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top