Daga Aliyu Ahmad

Fitaccen jarumin barkwancin nan na finafinan Hausa, Mustapha Badamasi wanda aka fi sani da Nabraska ya bayyana cewa ya bar harkar fim ne saboda cin zarafin da ake yi wa 'yan fim magoya bayan jam'iyyar adawa musamman wadanda suke goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Nabraska ya bayyana hakan ne biyo bayan kama abokin aikin su Darakta Sunusi Oscar da hukumar tace finafinan Hausa ta jihar Kano ta yi, wanda ya bayyana hakan a matsayin siyasa.

Nabraska ya kuma fitar da takardar sanar da daina yin fim a cikin jihar Kano, amma zai ci gaba da gudanar da harkokinsa na fim a sauran jihohi. "Ba zan sake yin fim a Kano ba har sai wannan gwamnati mai ci ta sauka daga mulki. Ko kuma idan Allah ya yi ikon sa a kotu. "Na yanke wannan hukunci ne saboda hukumar tace finafinai ta Kano tana amfani da ra'ayinta na siyasa, inda take ganin tana karkashin ikon APC. "Kano jiharmu ce, a nan aka haifi iyaye da kakanninmu. Ba wai bakin haure ba ne mu. Don ita Kanneywood wata kungiya ce wadda mutum ya sa kan sa a ciki, amma sai ake fakewa da ita ana cin mutunci jama'a, shine ya sa na fita daga cikinta domin na samu 'yancin ci gaba da gudanar da harkoki na fim a wajen jihar Kano. "Don haka yanzu a shirye nake da duk wani shugaban tace finafinai da zai zo ya tare ni. Saboda ba na shakkar wanda ba ya jin tsoron Allah", cewar Nabraska.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top