Daga cikin gargaɗin da sabon Ministan kula da harkokin sadarwa na Nageriya, Dakta Isah Ali Ibrahim Fantami ya yi a hukumarsa jiya, ya hori ɗaukacin ma'aikatan wannan hukuma da su kauda batun ƙabilanci cikin ayyukansu.
Ma'ana:
"Ku mu haɗa kai, mu girmama addini, yare da aƙidun juna, mu zauna lafiya mu yi wa ƙasarmu aiki".
"Wanda duk ba addininmu ko ƙabilarmu ɗaya ba, ka da su yi tunanin fuskantar wata tsangwama daga gare ni".
Kusan a iya cewa waɗannan saƙonni da wasunsu, mai girma Minista ya isar a dunƙule.
Kuma ba shakka wannan gargaɗi saƙo ne mai kyau, idan mu ka yi duba da yadda batun ƙabilanci da ƴangaranci ya ke taka rawa wajen daƙushe cigaban al'umma da rura wutar gaba a tsakani.
Ta yadda za ka ga ana hana mutum wata dama saboda shi ba ɗan wata ƙabila ko wani gari ko wani yanki ba ne.
Haƙiƙa, malam ya kyauta da ya yi wannan gargaɗi. Ko ba komai za a samu sauƙin wannan ɗabi'a a ma'aikatarsa.
Haka zalika, su ma ma'aikatan da su ka sha bamban da shi ta fuskar addini yanki da yare, kuma su ke da tunanin ko za su fuskanci tsangwama daga Malam to su ma za su saki jiki da shi a sanya ƙasa a gaba a hidimta mata.
Allah ya yi masa jagora.
-Garba Tela Haɗejia
Alhamis, 22/8/2019.
©HausaLoaded
Post a Comment