**

*Kasancewar wayar android itace akafi amfani da ita ynxu kuma zakaga kusan kowacce akan rufeta da password ko pattern Wanda mai ita kadaine ya sansu shi kadai zai iya budeta. To misali idan wayarka ta fadi, ko kuwa ka kasance cikin wani yanayi kaman na rashin lafiya ko hadari akan hanya kuma Wanda ya dauki wayanka yanaso ya kira wani Dan uwanka domin sanar masa halin da kake ciki, kuma sai ya kasance wayanka yana rufe ya kenan?... To kwantar da hankalinka domin ka samu mafita domin kuwa kusan kowacce android har wacce take hannunka yanxu takanzo da wani ilmi ( technology) Wanda zai bawa Wanda ya dauki wayanka damar ganin numba da sunan Wanda kakeso a kirawo, haka kuma koda kana kan wasu magani zaka iya rubutawa Wanda zaa iya nemosu da gaggawa domin tseratar da rayuwarka...Ga yadda ilmin yake...*

 *Yayin da wayanka ke rufe zakaga wani wuri an rubuta EMERGENCY a karkashin daidai inda zaka rubuta password dinka sai ka danna bayan ya shiga zaka kara ganin wani wuri an rubuta EMERGENCY INFORMATION sai ka danna da sauri sau biyu zakaga ya bude maka inda zaka zabi sunan mutane masu muhimmanci a rayuwan kuma ka ajiye numbansu da sunansu a wurin,,,,haka kuma akwai bangaren da zaka rubuta sunan magungunan da kake sha, blood group naka koda zaka bukaci jini da gaggawa,, sannan kuma zaka iya rubuta address naka wato unguwar da kake da zama*

*Don girman Allah yan uwa a turama wasu groups din domin ilmin ya kai ga yan uwa, wannan zai iya sanadiyar ceton ran wasu*

*IDAN KUN KARANTA KUYIMIN ADDUA TA ALKAIRI,,INA FATAN ALLAH YA GAFARTAWA DUKKAN WANDA YA SANARMA DA YAN UWA, YA ALLAH KA JIKAN MAHAIFANSA, KA YALWATA ARZIKINSHI, KA TSAWAITA SHEKARUNSHI A BAYAN KASA SANNAN KA SANYASHI A ALJANNARKA MADAUKAKIYA..AMIN THUMMA AMIN*





© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top