Sabuwar jaruma Maimuna Abubakar, wadda a ka fi sani da suna Momee Gombe a masana'antar fina-finai ta Kannywood, wadda za a iya cewa ta shigo harkar da kafar dama, domin kuwa duk da ba wani lokaci mai tsawo ta yi ba, kuma ga yadda masana'antar ta ke ciki, sunan ta a kullum sai kara dagawa ya ke yi kuma da alamanan gaba kadan za ta iya shiga sahun manyan jarumai.

A tattaunawarta da majiyar Northflix, jarumar ta bayyana tarihin ta da kuma yadda ta shigo harkar fim, inda ta fara da cewa.

"Ni suna na Maimuna Abubakar, amma an fi sa ni na da Momee Gombe a cikin harkar fim. Ni 'yar asalin fulani Gombe ce, a can na yi makarantar firamare da Sakandare kuma rayuwa ta ma tun da na taso a can na ke, daga baya ne na dawo Kano gidan wata' yar uwa ta”.

Dangane da yadda ta shiga harkar fim kuwa cewa ta yi "Ni daman tun ina karama ina da sha'awar harkar fim sosai, to da na dawo Kano ne na samu damar shiga harkar, duk da dai da farko ita 'yar uwar tawa ta nuna rashin amincewa, saboda ta ce harka ce ta marasa mutunci, amma dai daga baya ta amince, kuma daman na san Usman Mu'azu, domin haka na same shi ya yi mun hanyar shiga. kuma Usman Mu'azu shi ne ya sa ni na shigo harkar fim".

Dangane da tsawon lokacin da ta shafe zuwa yanzu kuwa da kuma yawan fina-finan da ta yi, jarumar ta ce " To gaskiya ba zan wuce shekara biyu zuwa da rabi ba, kuma fina-finan da na yi za su kai hudu zuwa biyar, kuma a cikin su fim din da na fara fitowa a matsayin jaruma, shi ne ‘Kishin Mata’.
Ko kin fuskanci kalubale a farkon shigowar ki harkar, musamman ma lokacin da a ka fara saka ki a fim?

" Gaskiya lokacin da a ka ce zan yi fim, abun ya dan tsorata ni kadan, amma da ya ke ina da karfin gwiwa a kan abun da na sa a gaba, sai kawai na dage har na samar da abun da ake so a cikin gurbin da a ka sa ni".
Mun tambaye ta dangane da surutun da ake yi a kan jarumai musamman mata cewar su ba zubar da mutuncin su da ma na harkar fim baki daya.

Sai ta kuma ce" Eh gaskiya sai dai idan mutum ba fim din ya zo yi ba, ka san shi mutunci mutum ne ya ke kare abun sa da kan sa, ba wani ne zai kare masa ba.Idan har ka zo da niyyar sana'a, to za ka yi sana'ar ka lafiya ka tafi, idan kuma ka zo da wata niyyar ta daban to ya rage naka, to kawai wasu matan da ba fim din su ke yi ba, su ne su ke shigowa su ke bata mana suna". Inji jaruma Momee Gombe.
Daga karshe ta yi fatan Allah ya daukaka ta ya kai ta duk wani matsayi da manyan jarumai su ke kaiwa, kuma ya raba ta da harkar fim lafiya.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top