Auren mata da yawa ya zama tamkar ruwan dare a wannan lokacin, sai dai kuma Dr. Aa’ed Al-Qarni, wani shahararren Malamin addinin Musulunci a kasar Saudiyya ,ya bayar da fahimtarsa dangane da auren.

Wannan magana ta Malamin ta jawo kace-nace da yawa tsakanin al’umma.

Al-Qarni ya ce mace daya ta ishi kowanne mutum rayuwar duniya, ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi a gidan talabijin na MBC. Wannan magana da Malamin yayi ta bawa mutane da dama mamaki, ganin ta fito daga bakin masani irin shi, kuma shima an san cewa yana da mace fiye da guda daya. Hakan ya sanya maganar tashi ta rikita wasu mutane da dama.

Al-Qarni ya cigaba da cewa duk da cewa Musulunci ya amince mutum ya auri mace fiye da daya a lokaci, amma hakan ya zo da sharuda.

Ya ce dole maza su koyi yadda zasu zauna da mace guda daya. Maganar da tazo da auren mace fiye da daya a Musulunci akwai rudani da yawa a ciki da ya kamata ace anyi gyara a kansu.

Ya bayyana cewa Musulunci ba wai ya halatta auren mace fiye da daya bane saboda kawai jin dadi na rayuwa, Musulunci ya halatta auren mace fiye da daya saboda yawaitar zawarawa da marayu da suke shiga cikin wani hali saboda rashin uba.

Auren mace fiye da daya ya samo asali ne saboda a dinga taimakawa wadannan mutanen da suke neman taimako, kamar yadda Musulunci ya koya mana duk wata hanya da zamu tafiyar da rayuwar mu.

Idan har ka san zaka iya daukar nauyin bazawarar da marayunta, sai ka aureta, saboda kada kowa ya manta sharadi na farko shine dole kayi adalci a tsakanin matanka.

Ayar da aka saukar domin auren mace fiye da daya an saukar da ita ne ga Annabi Muhammadu (SAW) bayan yakin Uhud. A wannan yakin Musulmi da yawa sun mutu kuma sun bar zawarawa da da marayu da yawa.

Daga baya aka saukar da Ayar cewa duk wanda za su iya daukar nauyin wasu su taimaka su auri matayen da mazajensu suka rasu.

 
Wannan ya tabbatar mana da cewa ba wai an halatta auren saboda jin dadi bane, an halatta shine saboda a taimakawa masu bukatar taimako.

Abinda Dr Al-Qarni yake nufi a nan shine, ka nesanci kanka daga auren mace fiye da daya, har sai lokacin da auren ya zama tilas a kanka. 

Mutane da yawa sunyi maganganu da yawa akan wannan magana tashi, haka kuma da yawa sun goyi bayan shi.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top