Duba da irin yadda ce-ce-kuce da ya ke yawa a kafafen sadarwa na sada zumunta wato social media, dangane da yadda jarumai mata matasa ke shiga a yanzu wadanda wasu ke ganin bai dace ba, shi ya sanya majiyar mu ta Northflix ta tattauna da jarumai mata iyaye domin jin ra’ayin su da kuma yadda za a yi maganin abun.
Ko kin san ce-ce-kuce na irin shiga da jarumai mata na Kannywood ke yi yanzu, wanda mutane da dama su ke ganin ya sabawa addini da kuma al’adar Hausa Fulani? Wanna ita ce tambayar da wakilin mu ba Northflix ya yiwa Haj. Hadizan saima. Sai ta fara da cewar ”wannan matsalar ba iya jarumai ba ce a yanzu gaskiya sai dai a ce tabarbarewar tarbiyya wanda kuma a ke fama da shi a duniya baki daya, zan iya cewa abun ya zama ruwan dare gama duniya, wanda zamani ya zo da haka da kuma irin tarbiyar da mace ta fito da shi daga gidan su. Idan yarinya ta fito da tarbiyya mai kyau daga gidan su babu yadda za ayi ta fito waje ta dauki tarbiyyar wata ta dora a kanta, kowa tarbiyar gidan su ya ke bi kuma yanayin shiga ita ke nuna yanayin tarbiyar gidan ku. Wasu kuma ba haka ma tarbiyar gidan na su ta ke ba, watakila iyaye sun yi iya bakin kokarin su daga karshe su ka zubawa sarautar Allah ido.
Kuma mu a bangaren mu nan Kannywood ta na iya bakin kokarin ta wajen ganin ta yi yaki da wannan abun a cikin ‘ya’yanta, kuma Alhamdulillahi ana samun nasara domin zan iya cewa kaso saba’in (70%) an samu nasara maimakon a ce abu yana karuwa sai dai raguwa, Alhamdulillah”.
Hajara Usman (Mama Hajjo) cewa ta yi “Ni a ganina rashin shugabanci kamar yadda na fada a baya, domin idan a ce muna da jagoranci to da duk hakan ba ta faru ba. Amma matsalar da mu ke samu kowa ya na cin gashin kansa, karami ba ya mutunta na sama da shi inda ana samun jagoranci kuma kowa ya na bin abun da na samansa ya fada to da idan aka saka doka dole a bi kuma ayi amfani da shi komai dadin sa ko rashin dadin sa“. A cewar Hajara Usman.
A ra ayin Maryam ctv cewa ta yi “Ba a iya fim ake samun wannan matsalar ba zan iya cewa wannan ta zama ruwan dare ko ina aka shiga yanzu yara sai dai addu’a kawai, zamani ne Allah ya kawo mu domin haka. Idan ka ga yaro ya na abu ba daidai ba to tsakanin ka da shi nasiha ce ko addu’a, kuma matsayin mu na iyaye mu na nan mu na ta addu’a” inji Maryam CTV
©HausaLoaded
Post a Comment