Tsohuwar jarumar fim din Hausa, Hadiza Muhammad Sani, wadda a ka fi sani da suna Hadiza Kabara, jaruma ce da aka dade da sanin ta a masana'antar fina-finai na Kannywood, sama da shekaru 17 da suka gabata, ko a wancan lokacin ta na cikin jarumai mata da su ke a sahun gaba, domin kuwa a wancan lokacin, ta kai matakin da idan babu ita a cikin fim to masu kallo su na ganin fim din bai kai matsayin babban fim ba, domin haka za a iya daukar Hadiza Kabara a matsayin jaruma ta sahun gaba a lokacin, sai dai ta na tsaka da tashen na ta su ka yi aure da uban gidan ta Muhammad Garba Kabara, sai dai auren na su bai je ko'ina ba su ka rabu bayan sun yi haihuwa daya tare. Daga nan ta kara dawowa cikin harkar fim, sai dai kuma dawowar da ta yi ba ta karayin wani tasiri ba, har zuwa wani lokaci da ta kara yin wani auren, kafin daga baya ta kara fitowa bayan a can ma ta kara haihuwa.
A yan watannin nan ne kuma a ka kara ganin fuskar Hadiza Kabara a cikin harkar fim bayan tsawon shekaru da ta yi ba a ganin ta, domin duk wanda ya kalli fim din Gidan Badamasi, zai tuna da Hauwa, sannan kuma Idan ba ka gane ta ba a nan to za ka gane Lantana mai adashi ta cikin shirin Dadin Kowa.
Saboda yadda a ke ganin Hadiza Kabara din ta dawo harkar fim mutane su ke tambayar daman tana nan? Wannan ce ta sa mu ka nemi jin ta bakin ta dangane da yadda ta dawo harkar fim a yanzu bayan lokacin ta da ta ci a baya, in da ta fara amsa mana tambayar da cewa.
"To daman harkar fim ina cikin ta kuma ban bar ta ba, domin ita na ke yi tun ina yarinya, domin haka ko a baya da ba a gani na, ina zaman aure ne, amma yanzu da ba ni da aure ka ga sai na dawo na ci gaba da harkar kafin Allah ya kawo mijin auren. Kuma daman tun da mu ka shigo harkar fim mun dauke ta ne a matsayin sana'a, domin haka idan na dawo sana'ar da aka sanni da ita ka ga ai ba wani abu ba ne, ka ga haka ni 'yar fim ce kuma fim sana' a ta ce, na samu duk wani rufin asiri na duniya ta harkar fim".
Dangane da tsawon lokaci da ki ka yi ba kya yin harkar, ko me ya sa ki ka dawo?
"To gaskiya ni na dauka harkar fim abu daya ne, Ko da ya ke dai an samu bambanci sosai da lokacin baya da kuma yanzu, domin ka ga a yanzu ma fim din an fi yin na Gidan talbijin mai dogon zango, sabanin a da da a ke yin fim na kasuwa, don haka ka ga an samu canji. Kuma a wancan lokacin an fi yin fim din ma da yawa, sabida za ka ga kowa ya na ta aiki, amma yanzu babu aikin kamar da". Inji jarumar.
Ko yaya rayuwar ki ta kasance da kika dawo ganin cewar kusan duk wadanda su ke yin harka a yanzu, kannen ki ne kuma ba ku san juna ba?
"To haka ne, amma dai babu wata matsala da na samu, domin idan na shiga cikin su su na girmama ni, kuma ita harka daman idan ka tsare mutuncin ka to babu wanda zai yi maka abin da bai kamata ba, domin haka mu na zaman Lafiya da su, sai dai abu daya da ya ke sa ni tunani, shi ne duk kusan wadanda mu ka yi harka da su a baya, to a yanzu babu su, sai wadanda su ka zo daga bayan mu".
An baya ki na fitowa a matsayin jaruma budurwa, kuma a yanzu kin kai matakin da ba za a saka ki a matsayin budurwa ba, ko ya ya ki ke ji? "To daman haka ne, a wancan lokacin mu ne 'yammata da a ke ya yi, amma a yanzu sai dai a ba ni na uwa ko yaya, domin haka ne ya fi dacewa da ni, saboda na yi girman da ba zan fito a matsayin budurwa ba, domin haka babu wani abu da na ke ji, domin an ba ni rol din da ya dace da ni ne, haka ba wani abu ne na daban ba, duk cikin fim ne bukatar dai a yi abun da ya dace".
Ko ya ya zamantakewar harkar fim ta ke idan ki ka kwatanta lokacin baya da kuma yanzu?
"Ai akwai bambanci, domin yanayin ya canza su kuma mutanen sun canza, an samu wasu abubuwa da a baya babu su, wannan kuma abun ya shafi lokaci, amma dai abun da zan iya cewa shi ne, a baya harkar fim ta fi ta yanzu tsari, kuma an fi ganin mutuncin juna, an fi zumunci sosai a baya". A cewar jarumar
Daga karshe ko mene ne shawarar Hadiza Kabara ga abokan sana'ar ki?
'Eh ni dai shawara ta, ita ce masu harkar fim mazan su da matan su, su kasance masu son junan su da kiyaye mutuncin juna, su zama yan uwan juna, sabida harkar sana' ar kamar ana zaman 'yan uwantaka ne, kuma wani taimakon ma da za ka samu na gaggawa ba lallai ba ne ka samu daga' yan uwan ka na jini cikin lokaci, kuma ina fatan Allah ya hada kan mu ya ciyar da sana'ar fim gaba ". inji Hadiza Kabara


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top