***************************
Babu shakkah akwai mata da yawa wayanda da zarar sun dauki ciki nan take yake zubewa ba tare da ansan dalilin zubewar tashi ba.

Barin ciki na daga cikin matsalolin da ake fama da su a yau, wanda akwai abubuwa da yawa da ke kawo wannan matsalar daga ciki akwai:

1. YIN AIKIN KARFI: Babu shakkah yin aikin karfi na daga cikin abubuwanda ke kawo zubewar ciki.

Daga cikin wayannan aikin karfin akwai dinkin tela, na kawo sanadiyar jijjigewar bakin mahaifar macce, wanda kai tsaye yake haifar da budewar bakin mahaifa, idan bakin mahaifar ya bude ruwan da jariri yake cikinsu sukan ragu, raguwar na kawo lalacewar ciki da ma kawowa mahaifa illah.

2. SHAN MAGANUKKA: shaye-shayen maganukka barkatai na turawa ko na hausa ko na musulunci yana kawo lalacewar ciki.

3. YAWAN HAIHUWA: Yawan haihuwa na kawo wannan matsala domin yazo a ilmun nafs cewa, Duk lokacin da aka haihu mahaifa na kara rauni, haka sassan jikin da ke taimakonta.

4. RASHIN WADATACCEN ABINCI: Rashin samun wadataccen abinci ga me ciki, ko wanda baya gina jiki na kawo wannan matsalar.

5. RASHIN DAI DAI TUWAR JINI: Idan aka samu cewa jinin uwa da na jaririnta basu dai daita ba, shima yakan haifada wannan matsalar.

6. NAKKASAR MANIYI: Samun nakasa ga maniyyin namiji ko kwan macce, na haifarda rashin tsayawar ciki ko rashin shigarshi baki daya.

7. JINNUL_ASHIQ: Samuwar wannan ja'irin aljani yakan haifarda matsalar yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki baki daya.

ALAMOMIN DA KE NUNA CIKI ZAI ZUBE.
Da farko mai ciki zata fara samun ciwon mara mai tsanani daga bisani idan ciwon ya tsananta sai ciwon baya ya biyo.

To lokacin da macce taji wayannan alamomi kuma ba'a dauki mata ki ba, nan take zata fara fama da zubar jini a hankali a al'aurarta daga nan sai ya fara zuwa da yawa, har abinda ke cikin yakai ga zubowa.

Wacce take tare da Jinnul Ashiq kuma zata yi mafarkin tana kokauwa da wani namiji da zarar gari ya waye zata tarar da kanta cikin jini cikin ya zube.

MAFITA GAME DA ZUBEWAR CIKI

Ana iya dakatar da zubewar ciki, kafin ya zube ko kafin mahaifa ta bude ta hanyar daukar mataki kamar haka.

YIN JIMA'I: Ana so macce mai wannan matsala da zarar ta samu cikin ta ni sanci tarawa da mai gidanta har lokacin da ciki ya tsaya.

DAKATARDA YIN AIKIN KARFI: Tun daga lokacin da macce ta fara jin alamun ciki ya shigeta to ta daina duk wani aikin karfi har cikin ya tsaya.
 
Haka wacce take tare da wannan mugun Aljani zata iya neman tsabar habbatus Sauda, sai ta karanta Suratul Baqara gaba daya a cikin wannan tsabar, sai ta dinga hayaki a dakin da take kwana, kuma sai ta tsuguna kan hayakin ya dinga shiga jikinta, za ta rinka yin haka da safe da lokacin da lokacin kwanciya

ALAMOMIN DAUKAR CIKI.
Wasu daga cikin alamomin da ke nuna macce ta dau ciki akwai,

YIN HASKE DA KIBA
Da zaran mace ta dauki ciki, to kuwa za ta canja kamannu. 

Kome zamanta baqa, takan yi haske ta rika sheki. Takan kuma dan kara kiba ta yi mul-mul.

Wata alamar kuma ita ce, ta yawan zubar da yawu, da yin kumallo, wani lokaci ma har da amai, da yawan yin ciwon ciki.

ABIN DA YAKAMA KOWA MA YA LURA DA SHI.

Yana da kyau masu wannan matsalar su zama masu tawakkaki ga Allah (swt) su tuna cewa, tun ran gini tun ran zane.

Domin a cikin Al'qur'ani Mai girma Allah (swt) na cewa,

���ِﻠَّﻪِ ﻣُﻠْﻚُ ﺍﻟﺴَّ��َﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻳَﺨْﻠُﻖُ ﻣَﺎ ﻳَﺸَﺎﺀُ ﻳَﻬَﺐُ ﻟِﻤَﻦْ ﻳَﺸَﺎﺀُ ﺇِﻧَﺎﺛًﺎ ﻭَﻳَﻬَﺐُ ﻟِﻤَﻦْ ﻳَﺸَﺎﺀُ ﺍﻟﺬُّﻛُﻮﺭَ ﺃَﻭْ ﻳُﺰَﻭِّﺟُﻬُﻢْ ﺫُﻛْﺮَﺍﻧًﺎ ﻭَﺇِﻧَﺎﺛًﺎ ﻭَﻳَﺠْﻌَﻞُ ﻣَﻦْ ﻳَﺸَﺎﺀُ ﻋَﻘِﻴﻤًﺎ ﺇِﻧَّﻪُ ﻋَﻠِﻴﻢٌ ﻗَﺪِﻳﺮٌ 
MA'ANA
"Mulkin sammai da qassai gaba dayan su na Allah ne. Yana
halittar abinda ya so yana ba da kyautar mata ga wanda ya so yana kuma ba da kyautar ‘ya‘ya
maza ga wanda ya so, ko ya hada wa mutum maza da mata ga wanda ya so, ko kuma ya bar shi bakarare (mara haihuwa). Lalle shi Allah masani ne kuma mai iko ne" (suratul Shuhra aya ta 50).

ZAUREN-MANAZARTA na addu'ar Allah Ubangiji ya Azzurta dukkan al'ummar musulmi da haihuwa.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top