Hukumar gudanar da zabe ta kasa wato INEC ta alanta da Alhaji Yahaya Bello na jam'iyyar All Progressives Congress APC matsayin zakaran zaben gwamnan da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2019.

Yahaya Bello ya lashe kuri'un kananan hukumomi 12 yayinda babban abokin hamayyarsa na PDP, Musa Wada, ya kashe kananan 11.

Baturen zaben jihar Kogi, wanda ya kasance shugaban jam'iyyar Ahmadu Bello ABU Zariya, Farfesa Ibrahim Umar, ya sanar da hakan Lokoja, babbar birnin jihar Kogi

Ya bayyana cewa Yahaya Bello ya samu jimillar kuri'u 406,222 yayinda Musa Wada na PDP ya samu kuri'u 189,704.

Kananan hukumomin da APC ta lallasa PDP sun hada da Okene, Okehi, Adavi, Olamaboro, Lokoja, Ibaji, Ajaokuta, Mopa Moro, Koton Karfe, Kabba Bunu da Ogori Magongo.



Kalli jerin sakamakon:

Karamar hukumar Okene APC: 112764 PDP: 139 SDP: 50

Karamar hukumar Okehi APC: 36954 PDP: 487 SDP: 3095

Karamar hukumar Adavi APC: 64657 PDP: 366

Karamar hukumar Omala APC - 8,473 PDP - 14,403 SDP - 567

Karamar hukumar Ijumu Ijumu LG APC - 11,425 PDP - 7, 587

Karamar hukumar Ogori/Magongo APC - 3,679 PDP - 2,145

Karamar hukumst Igalamela Odolu LG APC - 8,075 PDP - 11,195

Karamar hukumar Kabba/Bunu APC 15,364 PDP 8,084 SDP 364

Karamar hukumar Koton karfe APC - 14097 PDP - 9404

Karamar hukumar Yagba East APC - 6735 PDP - 7546

Karamar hukumar Mopa-Muro APC 4,953 PDP 3,581 SDP 95


Karamar hukumar Olamaboro APC 16,876 PDP 8,155 SDP 262

Karamar hukumar Idah APC - 4,602 PDP - 13,962 SDP - 221

Karamar hukumar Ajaokuta APC – 17952 PDP – 5,565 SDP – 323

Karamar hukumar Yagba West APC - 7,868 PDP - 8,860 SDP - 211

Karamar hukumar Ofu APC - 11,006 PDP - 12,264

Karamar hukumar Ankpa APC - 11,269 PDP - 28,108

Karamar hukumar Bassa APC 8,386 PDP 9,724

Karamar hukumar Dekina LGA APC: 8,948 PDP: 16,575

Karamar hukumar Lokoja APC 19,457 PDP 11,059

Karamar hukumar Ibaji APC: 12,682 PDP: 10,504

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top