- Masana kiwon lafiya sun bukaci jama’a da su yawaita cin ganyen gwaza

 - Yana dauke da sinadarai masu matukar amfani ga jikin dan Adam tare da bada kariya 

- Ana iya sarrafa ganyen gwaza kamar sauran abinci ta hanyar dafa shi ko miya da ganyen Masana kiwon lafiya sun bukaci jama’a da su yawaita cin ganyen gwaza. 

A cewarsu, yana dauke da sinadarai masu amfani ga jikin dan Adam. Bincike ya nuna cewa,

 ganyen gwaza na dauke da sinadarin kawar da cututtuka da suka hada da makanta, daji, hawan jini da sauransu. 

Ana iya sarrafa ganyen gwaza kamar sauran abinci ta hanyar dafa shi ko kuma miya da ganyen.

 A yankin arewacin Najeriya kuwa, ana dafa ganyen gwaza domin cin shi a haka, ko da manja ko man gyada ko kuma da miya.

 Ga kadan daga cikin amfanin gwaza a jikin dan Adam. 

1. Ganyen gwaza na kare mutum daga kamuwa da cututtuka saboda sinadarin ‘Vitamin C’ da yake dashi. 

2. Yana ba wa mutum kariya daga kamuwa da cutar daji kowacce iri.

3. Gwaza na kare dan Adam daga kamuwa da cutar sigari. 

4. Yana kara karfin jijiyoyin jiki har da mazakuta. 

5. yana taimakawa wajen nika abinci, kawar da ciwon ciki da hana yawan bahaya. 

6. Yana dauke da sinadarin ‘Calcium’ wanda ke kara karfin kashi da hakora. 

7. Ganyen gwaza na kare mutum daga kamuwa da hawan jini. 

8. Yana dauke da sinadarin ‘Folate’ wanda ke inganta girman dan ciki.

 9. Gwaza na inganta maniyyi a jikin maza. 

10. Yana kara jini a jikin mutum musamman ga yara kanana.

 11. Tana maganin yunwa.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top