Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi
Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano
Jarumar finafinai a masana'antar kannywood, da kuma Nollywood Hajara Isah Jalingo, za a iya cewa ta na daga cikin 'yan fim daga Arewa da su ke fitowa a cikin finafinai na kudancin kasar nan Wanda a ke Kira da finafinan Nollywood, domin kuwa ta yi finafinai na turanci da dama, kuma hakan ya sa a ke yi mata kallon,' yar fim din Arewa da ta ke wakiltar bangaren a kudu
Baya ga haka ta yi finafinai a kannywood masu yawa, kuma ko a nan Arewa din ma a fim na turanci na kamfanin Jammaje wato "There' s a way", Light and Darkness, wadda ta zama ita ce Jarumar finafinan duka.
Wakilinmu Mukhtar Yakubu, ya tambaye ta ko akwai wani bambanci da ke tsakanin finafinan kuda da kuma na Arewa?
Sai ta ce" To ko akwai wani bambanci ma dai bai wuce na yare ba, domin kuwa shi na kannywood da Hausa a ke yi, shi kuma na kudu da turanci a ke yin sa, idan ma akwai wani bambanci, to sai dan abin da ba a rasa ba, Wanda ya shafi bambancin Addini domin ka ga mu a nan Arewa, duk abin da za a yi a fim, to sai an kalli yanayin al'adar mu da kuma addinin mu, to a nan bambancin ya ke shigowa".
Amm da mu ka tambaye ta, ko me ya sa ba a cika ba ta rol mai karfi ba a finafinan kudu?
Sai ta ce, To gaskiya ina ganin ko don Saboda ba kowanne rol zan Iya yi ba, domin misali idan aka ba ni rol a finafinan kudu Wanda bai dace da addini da al'ada ta ba, ba zan yi ba.
Ta yiwu idan har zan fito ba za su ba ni babban rol ba wanda Duniya za ta sanni har sai na yi irin shigar da ba ta dace ba, ni kuma a matsayi na na musulma ba zan yi fim din da zan nuna tsiraici na ba.
Don haka duk wani fim na turanci da ya shafi kannywood zan yi shi, sannan na Nollywood ma idan bai saba wa addini da al'ada ta ba to shi ma zan yi".
Daga karshe ta yi Kira ga abokan sana'ar ta 'yan fim da su rinka kiyaye mutuncin su a duk lokacin da mu'amala ta hada su da mutanen da ba wajen zaman su daya ba.
Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya
©HausaLoaded
Post a Comment