NA
Mustapha Ahmad Khalid Kura
©Hakkin mallaka(m) Mustapha Ahmad Khalid Kura 1427=2006
GSM: 08036448209, 08032828495, 08023977728, 07025410254.
E-mail: mustaphakura@yahoo.com
Doka :-
Ba a yarda wani ko wata ya yi amfani da wannan littafi ba ta dauka a kaset ko sake buga shi ,ko sarrafa shi ta kowacce irin hanya ba tare da izinin mawallafin wannan littafi ba, a rubuce. Don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Na sadaukar da wannan littafi ga dukkan wata amarya da ta yi aure don neman yardar Allah, da bin sunnar Annabi S.A.W
BUGU NA FARKO:-
@ KUMURYA PRINTS U/UKU, B/LAYI 08036825943, 064-338984 KANO.
ABUBUWAN DA KE CIKI
(a) Sadaukarwa
(b) Gabatarwa
(c) Abubuwan da ke ciki
(d) Muhimmancin Aure a rayuwa
(e) Nau’ikan Maza
(f) Wacce irin mace ce ke?
(g) Daren budar kai
(h) Hakkohin miji a kan matarsa
(i) Nasihohi ga Amarya:
   1-Zaben miji nagari
   2-Yi kwalliya ga miji
   3-Nuna kauna ga miji
   4-Kada ki cuci mijinki
   5-Fara’a ga miji
   6-Neman yardar miji
   7-Hanyar hira da miji
   8-Taya miji farin ciki
   9-Nuna wadar zuci
 10-Hakuri bisa talaucin miji
11-Kulawa dabakin miji
 12-kyautata wa iyayen miji
 13-kulawa da Hakkokin miji
 14-Amsa kiran miji
 15-Kada ki koda wata a gabansa
 16-Bndakafirce wa miji
 17-ki guje wa bacin ransa
 18-Banda barnatar da dukiyarsa
 19-rike sirrin miji
 20-Banda korafi
 21-Kada ki yi alfahri da kyanki
 22-Yaba wa miji da koda shi
 23-Banda gori
 24-Taimaka masa a hakokin gida
 25-Karfafa masa gwiwa don aikita alheri
 26-banda tuna mijin baya
 27-Banda mita
 28-Kada ki yi azumi ba da izininsa ba
 29-kada ki je unguwa sai da izininsa
 30-Banda yawaita fita unguwa
 31-Ki bi sharudan fita unguwa
 32- Banda tsiwa ga mijinki
 33-kada wani ya shigo gidanki sai da izininsa
 34-Idar da soko gare shi
 35- Zaman aure sai da ilimi
 36-ki tsaftace gidanki
37-kada ki yi fada da mjijnki a gaban ‘ya’yanki
38- Banda laluban aljihun miji
39- ki guji yin karya da gulma ga miji
40- tsaftar jiki da tufafi
41- banda aboki a waje
42- Banda ha’inci a gida ko waje
43- Kada ki matsa wa mijinki a wajen ciyarwa
44- Nemi yafewarsa idan kin masa laifi
45-kada ki boye masa laifin da ya yi maki
46-Taryar miji da walwala
47- Addu’a ga miji
48- Banda mummunan kishi
49- Banda zaman banza,nemi na kanki
50- Kada ki nemi saki
(j) A karshe
(k) Addu’o’in yaukaka zaman aure
(l) Manazarta
                        GABATARWA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki.Tsira da aminci su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad,da Alayensa Tsarkaka, da Sahbbansa masu gaskiya,da sauran Musulmai masu binsu har tashin kiyama.
Wannan littafi da ke hanun mai karatu daya ne daga litattafai uku da na rubuta su domin yin nasiha ga ‘yan uwa musulmi kamar dai yadda Manzon Allah S.A.W. ya yi umarni da yi a gare su.Yi wa Amarya da ango nasiha wani bangare ne na sasanta tsakanin ma’aura biyu,wanda Manzon Allah S.A.W. ya yi bushara da babban rabo ga wanda ya aikata haka.
 A gaskiya, a wannan zamani da muke ciki marubuta ba su cika bayar da karfi wajen wallafa litattafai ba, wajen riga-kafin magance yawan mace-macen aure da ya yi yawa ba,sun fi ba da karfi wajen dasa soyayya ta karya a zukatan ma’uara.
Abubuwan da na ambata a wadannan litattafai ban kure nasihohi ga su am’auratan ba. Na kawo su ne don su zama kamar mabudi da fitila ga ‘yan uwa da suke da sha’war fadada wannan fage na yaukaka zaman lafiya ga ma’aurata.Saboda haka na kira littattafan da sunaye kamar haka:
-NASIHOHI 50 GA AMARYA
-NASIHOHI 50 GA ANGO
-NASIHOHI 50 GA IYAYEN ANGO DA AMARYA
A karshe ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya albarkaci wannan aikin nawa, ya sanya shi karbabbe ga dukkan 'yan uwa musulmi,domin Shi Allah Mai iko ne a bisa dukkan komai.
          Dan uwanku
   Mustapha Ahmad Khalid Kura
7th Yuli 2006
            MUHMMANCIN AURE A RAYUWA
Allah Madaukakin Sarki ya yi magana a kan aure da muhimmancinsa a rayuwar bayinsa a wurare da dama a cikn Alkur’ani Mai girma.Daga cikinsu shi ne fadinsa S.W.T.يا ايها الناس اتقوا ربكم الذى خلقكم من نفس واحدة وخلق منها زوجها وبث منهما رجالا كثيرا ونساء) النساء\1
(Ya ku mutane ! Ku ji tsoron Ubangijinku, Wannan da ya halicce ku daga rai guda daya,kuma ya halitta daga gare shi matarsa ,kuma ya samar da maza da yawa da kuma mata da yawa ) Nasa’i/1
Allah ya samar da miji da matarsa ba wai kawai a cikin ‘yan Adam ba, a’a har a saran ababan halitta,dabbobi,tsintsaya,tsirrai da sauran ababan halitta,kamar yadda yakw cewa:
ومن كل شىء خلقنا زوجين لعلكم تذكرون ) الذاريات |49
(Kuma Mun halicci namiji da mace a dukkan komai,tsammaninkuku zama masu tunawa) Zariyat/49
Manzon Allah S.A.W. yana cewa “Aure sunnata ne, wanda yake son hanyata, to, ya sunnanta da sunnata.”Abu Ya’la daga Ibn Abbas
Ya sake cewa :- “Ya ku taron samari!Wanda zai iya ciyarwa a cikinku,to, ya yi aure,domin yana rintse gani,yana kiyaye farji,wanda ba zai iya ba, to, ya yi azumi, domin shi kariya ne”Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
                          NAU’IKAN MAZA
Kafin mace ta yi aure ya kamata ta san cewa maza irin gujiya ne, sai an fasa akan san na kwarai,ba kawai da ganin namiji ba don yana da sura ki amince za ki aure shi,ya kamata ki gane mazannan za su iya zama kamar haka:-
(1)Dantsako;wato samu ka ki dangi, mugun namijin da iyalinsa ba sa hutawa da shi, sai ya bar ‘ya’yansa cikin yinwa da ragga ,da ya samu kansa kawai ya sani,hakkin ciyarwa da tufatantarwa,da makamantan haka ba ruwansa da su.
(2)Ragon maza:-Ba shi da katabus,ya zuba ido komai a yi masa,bai san mayar da kwandala ta zama biyu ba,ba ruwansa da tarbiyar ‘ya’yansa ba ma ‘ya’ya mata,a wajensa ‘ya mace ta mace ce.Zuciyarsa a mace take,komai nasa ya barwa matarsa,ta yi ko kada ta yi duk daya.
(3)Dansharholiya:- Sau da yawa zaka same shi addini bai da me shi ba,bar shi dai wajen holewa da shakatawa,da sharholiya,duk abin da ya samu na matan waje ne, bariki kawai ya sa a gaba.
(4)Miji na gari:-Shi ne mai tsoron Allan kokarinsa sauke nauyin da yake kansa na hakkokin matarsa da na ‘ya’yansa da sauran al’umma.Ya dauki matarsa a matsayin masoyiya, abokiyar rayuwa, wadda Allah ya yi umarni da a kula da ita kamar yadda ake kulawa da kwan kaza a cokali kusa da dutse.Shi ne wanda ya damu da tarbiyar ‘ya’yansa da kulawa da gidansa ,mai kokarin kare kansa da iyalinsa ga barin shiga wuta, kamar dai yadda Allah ya yi umarni.
                  WACCE IRIN MACE CE KE?
Mace tagari ita ce ma’abociyar addini,mai kyawawan halaye,kyakkyawa, mai saukin kai, mai saukin sadaki,budurwa ce ko bazawara,ga ta mai haihuwa ,mai dangi,da bin Allah sau da kafa.
Baya ga wannan akwai wasu matan da suka saba wa wannan halin da dabi’ar,wadanda ma iya kiran su da sunan mugwayen mata, wadanda ake fatan za ki nesanta kanki da su.Irin wadannan matan sun hada da:-
(1)Mace mai yawan mita da gori ga mijinta.
(2)Mai yawan alhini a kan mijinta na baya ko ‘ya’yanta da ta bari a wani gidan.
(3)Mai sanya ido a kan harkokin mijinta ,ta dora masa abin da ba shi da iko a kai.
(4)’Yar kwalisa, sai ta wuni ta yin kwalliya ,shafa wancen ,goge can,tun safe har sai rana ta yi, ba don ta burge mijnta ba, a’a sai don zata unguwa ,wasu mazan su ganta su ce ta burge, ko don ta janyo hankalin wasu mazan.
(5)Mai kwadayi: Ba ko wane abinci ta ke ci ba,ta fi ga kayan dadi ,ga kwadayi kamar mayya,ga rowa,kamar yaron goye.
(6) Mai yawan surutu
(7)’Yar dandane:-Ita ce wadda ba ta zaman aure,daga wannan mijin sai wannan,a shekara guda sai ta yi aure uku ko fiye,koda yaushe ita dai neman mjinta ya sake ta,da laifi ko ba laifi.
(8)Mai son abin duniya,ita dai kudi, komai zai faru ya faru indai za ta sami kudi.
(9)Fasika,mai neman maza.
(10)Mai nuna isa da son fin karfin miji
(11)Mai yawan tsegumi da asirce-asirce.
       ‘Yar uwa da wasu mugwayen matan,kada ki yarda ki zama daya daga cikin wadannan mata,ki yi hattara sai ki rabauta.
                     DAREN BUDAR KAI
Bayan an daura aure,amarya ta tare,a daren da mijnta zai fara kwana a wajenta, akwai wasu bakin abubuwa da za ta fara gani wadanda ba ta saba da su ba,bisa haka ne ake yi mata nasiha da wadannan abubuwan masu zuwa:
a- Kada ta nuna wa mijinta tana jin tsoron abin da zai faru tsakaninsu a wannan daren.
b- Ta kiyaye sirrin abin da ya faru a tsakaninsu,kada ta bayyana wa kawaye , ko wasu,yin haka barna ce babba,kuma Allah zai kwashe albarakar auren naki.
c- Kada manya su rika shiga wajen amare koda yaushe, ba ma a watan amarci,don gudun hana musu sakewa.
d- Ana son ango da amarya kowannensu ya nuna gamsuwa da juna,koda kuwa dayansu ya sami matsala wajen biyan bukatarsa.Don akan samu a daren budar kai wani angon ba ya iya tara da matarsa saboda wani dalili,kada amarya ta dauka ba shi da lafiya ne,ko baya son ta, kamar yadda shi ma mijin zai iya samun wannan matsalar awajen amaryarsa.
e- Kada a fara saduwa kai tsaye sai an bi wadannan matakan:-
-Yin salla raka’a biyu,da yin addu’ar fatan alheri a tsakanin juna, ba kamar wadda Manzon Allah S.A.W.ya koyar.Duba karshen littafin
-A sami wasanni da nishadi kafin saduwa.
-Yin addu’ar da Annabi S.A.W.ya koyar wajen saduwa.
      d-Yawan shan magungunan kara ni’ma ga mace ko kara karfin maza rashin amfaninsa ya fi amfaninsa yawa don haka a kiyaye.
        HAKKOKIN MIJI A KAN MATARSA
1-Biyayya gare shi,kamar yadda Manzon Allah S.A.W.ya ce”Idan mace ta sallaci salloli biyar dinta,ta azumci watanta,kuma ta kiyaye farjinta,kuma ta bi mijinta,za ta shiga aljanna”
2-Kiyaye mutuncinsa, da dukiyarsa,Manzon Allah S.A.W.yana cewa “Bana ba ku labarin abin da ya fi kyau mutum ya taskance shi ba?Mace tagari,idan ya dube ta sai ta sanya shi farin ciki,idan ya umarce ta sai ta yi masa biyayya,idan ba ya nan sai ta kiyaye masa kanta da dukiyarsa”
3-Kulawa da hakkokin miji da tarbiyar yara,har ma da dafa abinci da gyara wajen kwanciya.An ruwaito cewa Sahbban Annabi sun kasance idan suka raka ago wajen amaryarsa, suna yi mata nasiha da ta bi mijinta kuma ta yi masa hidima ta kula da hakkokinsa ta yi tarbiyar ‘ya’yansa.
4-Kada ki kaurace masa wajen wajen kwanciya,Manzon Allah S.A.W.ya ce “idan mace ta wayi gari tana mai kaurace wa shimfidar mijnta, Mala’iku za su yi ta tsine mata, har sai ta tuba “.
          NASIHOHI GA AMARYA
Yin nasiha ga amarya wajibi ne,bisa koyarwar Alkur’ani Maigirma,da Sunnar Annabi S.A.W.
Manzon Allah S.A.W.yana cewa:”Ku yi wa mata wasiyya da alheri,domin mace an halicce ta daga kashin awaza karkatacce,mafi karkatar awazai na samansa.Idan ka yi niyyar mikar da shi sai ya karye,idan ka bar shi, sai ya zauna a karkace,ku yi wa mata wasiyya da alheri “Bukhari da Muslim suka ruwaito.
A wani hadisin Manzon Allah S.A.W.yana cewa: “Hakika mace an halicce ta daga awaza har abada ba za ta mike kan hanya ba ,idan ka ji dadi da ita, ka ji dadin ne da ita tana da karkata,idan ka yi nufin mikar da ita sai ka karya ta , karya ta kuwa shi ne sakinta” Muslim ne ya ruwaito.
Bisa haka ne za mu gabatar da wadannan nasihihi ga AMARYA.
(1) ZABAR MIJI NAGARI
Ki zabi miji nagari,domin rayuwar aure tana bukatar fahimta, kauna,da tausayin juna.
A wajen zabar mijj ana gabatar da addini a kan dukkan komai,domin idan addininsa ya gyaru rayuwar aure za ta cika da tsoron Allh, da kyautatawa tsakanin juna.Manzon Allah S.A.W.yan cewa: “Idan wanda kuka yarda da addininsa da halayensa ya zo muku {don neman aure }to ku aure shi, idan ba ku yi haka ba , fitina da fasadi za su yi yawa{a ban kasa}” Tirmizi ne ya ruwaito.
(2)YIN KWALLIYA GA MIJI
Mace ta kasance cikin tsafta ,da kwalliya koda yaushe na sanya miji cikin jin dadi da kwanciyar hankali,don haka Manzon Allah S.A.W. yake cewa:”Babu wani abu da mumini zai amfani da shi bayan tsoron Allah fiye da mace tagari, idan ya kale ta sai ta faranta masa rai”Tirmizi ne ya ruwaito.
(3)NUNA KAUNA GA MIJI
 Nuna wa mijinki kauna wani bangare ne na ibada,wanda hakan kan sanya yarda da soyayya a tsakanin juna.Manzon Allah S.A.W.ya so Nana Khadaja, ba don komai sai don irin son da ta nuna masa tun kafin da bayan ya zama Annabi.
Kada ki yarda da fadin da da kake cawa wai idan mace ta cika nuna so ga mijinta zai wulakanta ta.
 (4) KADA KI CUCI MIJNKI
Manzon Allah S.A.W yana umartar mace da kada ta cuci mijinta ,yana cewa: “Ba wata mace da za ta cutar da mijinta a duniya, sai matarsa ta gidan Aljanna ta ce Allah wadanki,kada ki cutar da shi, shi fa bako ne gareki ya kusata ya bar ki ya dawo garemu”.
                (5)FARA’A GA MIJI
Sakin fuska,da walwala, da yin fara’a ,alma ce ta nuna yarda da kauna ga miji,don haka ma Hausawa suke cewa labarin zuciya a tambayi fuska.Manzon Allah S.A W yana cewa:”Kada ka wulakantar da wani abu daga abin sani,ba ka fuskanci dan uwanka da sakakkiyar fuska ba”
(6)NEMI YARDAR MIJINKI
Babban abin da masoya biyu ke fatan samu a tsakaninsu shi ne yarda da juna, da amince wa juna.Wanda haka kan kara dankon zumunci da soyayya a tsakaninsu.Manzon Allah S.A.W. yana cewa:”Duk matar da ta mutu,mijinta yana mai yarda da ita,zata shiga aljanna.”
Wata mace mijnta ya rasu,sai ta yi mafarki bayan mutuwar tasa,ga shi a bakin kofar wani gida a cikin aljanna , sai ta tambaye shi,wannan gidan na waye?Sai ya ce da ita, naki ne ,ba wata mace da za ta shige shi bayan ke,saboda amincewar da na yi da ke.”
(7)HANYAR YIN HIRA DA MIJI
Ba ko wace irin magana da ta fito daga bakinki za ki yaba masa ba,ana son hirarku ta kasance cikn mutunci da girmama juna,ta hanyar sanyaya murya,da sakaya masa sunansa,kamar kice mai gida, ko msoyina,Abban wane,da makamancin haka,shi ma haka zai yi.
Matar Sa’idu Dan Musayyib ta ce; Mu muna yi wa mazanmu zance kamar yadda kuke yi wa sarakunanku,mu ce da su Yallabai, mai gida da sauransu.
(8)TAYA SHI FARIN CIKI KO BAKIN CIKI
Wajibi ne Amarya ta karanci halayen mjinta,ta gane lokacin farin cikinsa da lokacin bakin cikinsa, haka zai taimaka kwarai wajen samar da zaman lafiya a tsakaninki da shi.Ana son idan yana cikin farin ciki ta nuna nata farin cikin,idan kuwa wani abu ya bata masa rai, kada ki nuna farin ciki,ki nuna ma kin fishi damuwa da halin da yake ciki,kuma ki ba shi shawara ta gari,inda zai samu waraka a kan haka.
Umma ‘Yar Haris ta yi wa ‘yarta wasiyya lokacin da za a yi mata aure, take cewa:Ki guji yin farin ciki a lokacin da yake bakin ciki,ko kuma bata rai alokacin da yake farin ciki.
(9)NUNA WADATAR ZUCI
Wadar zuci ginshikin rayuwa tagari ce ga kowanne mutum, bama kamar matar aure.Wadatar zuci sufa ma da Allah S.W.T. ya suffanta matan aljanna da ita,inda yake cewa:
{ فيهن قاصرات الطرف لم يطمسهن أنس قبلهم ولا جان}
”A cikinsu akwai mata masu takaita ganinsu......”Al-Rahman/56.
Kada ki yarda ki dara wa mijnki abin da ya fi karfinsa, duk abin da ya kawo ya ba ki, ki karba ki ce kin gode Allah saka da alher, wata ran sai ya kawo wanda ya fi shi.
An ruwaito cewa:Matar gidan aljanna idan ta ga mijintasai ta ce da shi;Wallahi ban taba ganin wani abu mai kyau wanda ya fi ka kyau a gidan aljannar nan ba,kuma ba wani abu da na fi so fiye da kai,na gode wa Allah da ya sanya ka kai ne nawa,kuma ni ce taka.
(10)HAKURI BISA TALAUCINSA
 Wasu matan sau da yawa sun fi son su ji su cikin wadata ko da yaushe, Allah S.W.T. ya kan jarrabi bawansa da talauci bayan ya arzuta shi, ko kuma da talaucin ma gaba daya.
 Amarya ki zama mai hakuri bisa talaucin da Allah ya jarrabi mijnki da shi.
Nana A'isha R.A. tana cewa: "Iyalin Muhammad S.A.W. ba su ta ba koshi da gurasar sha'ir ba, kwana biyu a jeer, har Allah ya karbi abinsa.
 Ta cigaba da cewa: Wallahi ya dan 'yar uwata mun kasance muna jiran jinjirin wata, sannan wani jinjirin watan, sannan wani jinjirin watan, har jirajiran wata uku a wata biyu,ba a kunna wutar girki ba a gidan Manzon Allah S.A.W.
 Sai Urwah y ace : Ya 'yar Uwar Baba,to da me kuke rayuwa ?Sai ta ce: Bakaken abubuwa biyu,wato dabino da ruwa." Bukhari da Muslim ne suka ruwaito.
(11) KULAWA DA BAKIN MIJINKI
 Baki suna daya daga abubuwan da suke bunkasa rayuwar al'umma, don haka ne manzon Allah S.A.W. ya yi umarni da a girmama bako da mutunta shi, wanda yin haka ma alama ce ta imani da Allah da ranar lahira.Don haka kada ki wulakanta bakin mijinki,kowadanne iri ne.
(12) KYAUTATA WA IYAYEN MIJI DA DANGINSA
 Amarya ki kula da iyayen mijinki, domin iyayenki ne,ki kyautata musu ,ki mutunta su .Haka nan ma ki kyautata wa 'yan uwansa da danginsa ,sai mijinki ya so ki ya kuma kyautata maki,ya kuma girmama naki iyayen da dangin.
(13) KULAWA DA HAKKOKIN MIJI
  A baya mun bayyana wasu daga hakkokin mijinkia kanki, to wajibi ne gareki Amarya,ki san su ,ki kula da su, kuma ki aiwatar da su.Don ki sami yarda a wajen Allah da kuma wajen mijnki.
(15) AMSA KIRAN MIJI
 Ki zama mai amsa kiran mjinki a duk lokacin day a kira ki, kada ki yi shiru, domin yin haka wulakanci ne.Karewa ma idan ya neme ki don ya biya wata bukatarsa, kika ki amsawa, kin yi babban laifi,kamar yadda Manzon Allah S.A.W yake cewa:" Idan miji ya kira matarsa zuwa shimfidarsa ,ta ki zuwa,ya kwana yana fushi da ita, Mal'iku za su yi tat sine mata har ta wayi gari".Bukhari da Muslim
 Idan mace ta amsa kiran mijinta zuwa shimfidarsa za ta amfana da abubuwa uku:
a- Ta hana mijinta fadawa neman mata.
b- Ta sami rabonta, domin ita ma ta biya tata bukatar.
c- Mala'iku za su so ta ,kuma Allah ya ba ta lada.
(15) KADA KI KODA WATA MACE A GABAN MIJINKI
 Kada ki yarda ki yabi wata mace, budurwa ce ko bazawara a gaban mijinki,ta hanyar nuna ma tana da kyawawan halaye , iya kwalliya, ko iya Magana, ko ilmi,ko makamantan haka, ba don komai ba ,sai don kada zuciyarsa ta ta'allaka da ita.
 Manzon Allah S.A.W. yan cewa:"Kada mace ta hadu da wata mace hart a suffanta ta ga mijinta kamar yana ganinta."
            (16) BANDA KAFIRCE WA MIJI
 Ana nufin yi masa butulci, da rashin godiya bisa abin da mijin yake yi mata an alheri.Manzon Allah W.A.S. ya yi wa mata wa'azi, inda ya hane su da kada su kafirce wa mazansu,inda y ace:" Na ga wuta, sai nag a mafi yawan masu shigar ta mata ne." Sai Suka ce, saboda me ya Manzon Allah? Sai y a ce:" Saboda kafircewarsu".Aka ce: Suna kafirce wa Allah ne? Ya ce:"Suna kafirce wa abokin zama,kuma suna kafirce wa kyautatawa,da za ka kyautata wa dayansu tsawon zamani, sannan tag a wani abu gareka ,sai ta ce : Ban taba ganin wani abin alheri a tare da kai ba."Bukhari ne ya ruwaito.
(17) KI GUJI WA BACIN RAN MIJINKI
 Kada ki zama irin matan nan da su kullum burinsu su bata wa mazansu rai.Ki zama mai faranta masa rai.
Manzon Allah S.A.W. ya ce:” mutane biyu sallarsu ba ta wuce kawunansu :Bawan da ya guje wa mai gidasa, har sai ya dawo da matar da ta bata mijinta (kular da shi ) har sai ya sauka (ya daina fishin). Hikim ne ya rawaito
(18) BANDA BARNATAR DA DUKIYARSA
             Allah S.A.W. ya yi umani da yin tattali sanan ya haramta barna da
cewarsa
{والذين إذا انفقوا لم يسرفوا ولم يقتروا وكان بين ذلك قواما}الفرقان/65
(kuma da wanda idan suka ciyar ba sa yin barna, kuma ba su yin kwauro,kuma (ciyarwarsu)sai ta kasance a tsakanin wancan da tsakaitawa].
            Sau da yawa aure yana mutuwa saboda rashin tattalin matar . Don haka amarya ki yi tattalin dukiyarsa banda almubazzaranci.
(19) RIKE SIRRIN MIJI
           kowanne mutum yana da sirrinsa kamar yadda ango da amarya suke da nasu sirrin dan haka amarya ki boye sirrinsa kada ki yada shi.
          Manzan Allah S.A.W. Yana cewa:
"Mafi sharrin mutane a wajen Allah a ranar kiyama mutumin da ya kadaice da matarsa, ko tadaice da shi , sannan sai dayansu ya rika yada sirrin dan uwansu".Musulum ne ya ruwaito.
          Kamar yadda muka ambata a baya, kada ki bayyana yadda kuke da angonki a watan amarci ga kawaye ko 'yan uwa.
(20) BANDA KORAFI
          Rashin godiya yawan koke-koke, da yawan korafi halayyar wasu mata ne kada ki dauki wannan hali. Domin yin hakan fasikanci ne babban sabo ne. Manzan Allah S.A.W yana cewa: "Allah ba ya duban mutar dab a ta godiya ga mijinta, wadda ba ta wadatuwa da shi" Hakim ne ya rawaito
         Ya sake cewa a wani hadisin:" fasikai dai su ne yan wuta" sai suka ce ya manzan Allah su waye fasikai? Ya ce: "mata" suka ce ya manzan Allah su ba iyayenmu ba ne, da yayanmu dayan uwanmu. Ya ce: "Haka ne mana amma su sun kasance idan aka da su bas a godiya, idan kuma aka jarrabe su bas a yin hakuri: hakim ne ya ruwaito
(21) KADA KI YI ALFAHARI
Kyau na fuska da na jiki baiwa ce ta ubangiji da yake yin ta ga bayinsa. Amma kyawawan halaye su suka fi kowanne irin kyau daraja.
     Don haka kada ki yi alfahari da kyau da Allah ya yiu miki. Idan kina da kyau din ki kara da wanka, kamar yadda hausawa suke cewa.
(22) YABA WA MIJI DA KODA SHI
     Amarya|! A duk lokacin da mijinki ya yi wani abin arziki har ya burge ki, ki nuna masa. Ba ma kamar idan ya yi kwalliya ta birge ki. Ki ziga shi ki koda kice masa amma fa ka hadu, kayan nan sun maka kyau. Sai ya ji dadi ya kara san ki.
(23) BANDA GORI
      Allah S.W.T ya haramta gori, da cewarsa:
{ياأيها الذين ءامنوا لا ��بطلوا صدقاتكم بالمن والأذى....} البقرة/264
(Yaku wadanda kuka yi imani! Kada ku bata sadakokinku da gori da cutarwa) Bakara\264
            manzan Allah S.A.W ya ce: "mutane uku Allah ba zaya yi Magana da su ba ranar kiyama, kuma ba zaya dube su ba, ba kuma za ya tsarkake su ba, kuma suna da azaba mai radadi daga cikisu akwai mai yawan gori" musulum ne ya rawaito.
        Don haka wani mutum ya yi dansa wasiyya da kada ya auri daya daga matannan uku:
(a) Mai yawan tuna mijinta da ya mutu.
(b) Mai alhinin tuna danta da ta bari a gidan wani mijin.
(c) Mai yawan gori ga mijinta
(24) KI TAIMAKA MASA A HARKOKIN GIDA A kan sami wasu matan sunfi mazansu abin hanu, idan kina cikinsu amarya ki zama maitai maka masa da dauke masa nauyin wasu abubuwan, sai ya kara sonki.
      Ko da ma ya na dashi yan da kyau ki rika taimakonsa, a wajen cefane, kudin kudin makaranta da makamancin haka.
      Ummu salma ta je wajen Annabi S.A.W ta tambaye shi cewa: ina da lada idan na ciyar da 'ya'yan Abu salma (yayan mijita) domin su yayana ne? sai ya ce:"ki ciyar da su kina da ladan abin da kika ciyar". Bukahri ne ya rawaito.
      A wani hadisin ya ce "tana da lada biyu: ladan kusanci da ladan sadaka".
(25) KARFAFA MASA GWIWA DON AIKATA ALHERI
       Ki zama jagorar sanya mijinki a kan hanyar aikata alheri, kada ki jefa shi cikin aikata munanan ayyuka.
      Allah S.W.T yana cewa:
{وتعاونوا على البر والتقوى }المائدة/2
      (Kuma yi taimakekeniya a kan aikata alheri da tsoran Allah)Ma'ida\2.
Manzan Allah S.A.W yana cewa: "Allah ya ji kan wani mutum da ya tashi da dare ya yi salla, kuma ya tashi matarsa, idan taki tashi, sai ya yayyafa mata ruwa a fuska,(don tatashi). Allah ya ji kan matar da ta tashi da dare ta yi sallah, ta tashi mijinta, idan ya ki tashi, sai ta yayyafa masa ruwa a fuska (don ya tashi)"Abu Dawud ya rawaito.
(26) BANDA TUNA MUJIN BAYA
      Amarya ban da tuna mujun baya, ballantana har ma ki rika bayyana halayensa a gaban sabon mijinki, domin yin haka kan iya sa aurenku ba zai dore ba.
(27) BANDA MITA
        Wasu matan Allah ya yi su damita da binbinin Magana, kada amarya ki zama mai mita, domin don son da mijinki yake miki, za ki fita daga ransa yana ma ji ba ya son ganinki.
(28) KADA KI YA AZUMI SAI DA IZININSA
       Ba a son mace ta yi azumi nafila ba tare da izinin mijintaba, don zai iya yiwuwa yana bukatarta ita kuma tana azumi bai sani ba, sai ta fada cikin fushin Allah S.A.W.
        Manzan Allah S.A.W ya ce: bai halarta ba ga mace ta yi azumi mujita yana nan sai da izinisa"Bukari da muslim ne suka rawaito.
(29)KADA KI JE UNGUWA SAI DA IZININ SA
Fita unguwa ba ya yiwo sai da izinin mai gida. Idan mace ta fita ba da izininsa ba, ko ta yi satar fita unguwa, to tana cikin fishin ubangiji har sai ya yafe mata.
Wata mace taje wajen manzon Allah S.A.W tana tanatambayarsa ya manzon AllahS.A.W meye hakkin miji a kan matarsa? Sai yace: "kada ta fita daga gidanta sai da izininsa idan ta aikata, malaikun Allah za su tsinemata. Ibn Abdulbarri ne yaruwaito.
(30)BANDA YAWAITA FITA UNGUWA
Allah S.W.T ya umarci mata da su zauna a gidajensu, kada su yawaita fita ba tare da wani dalili mai karfi ba. Don haka yake cewa:
{وقرن ف���� بيوتكن ولا تبرجن تبرج الجاهية الأولى..} الأحزاب/33
       (kuma ku tabbata a gidajenku kada ku fita irin fitar jahiyyar farko)Ahzabi/33.
Sannan manzan Allah S.A.W yana cewa: "mace al'aura ce idan ta fita (unguwa) sai shaidan ya rakata" tirmizi ne ya rawaito.
(31) KI BI SHARUDAN FITA UNGUWA
        Idan fita unguwa ya zama wajibi gareki amarya ki tabbatar kin bi sharadan da sari'a ta shimfida wajen fitar mace kamar haka:
          (a)banda yiun kwalliya.
          (b)banda fitar da irin tufafin da aka sanya atamfa ce, ko shadda damakamantan haka. (c)banda sanya turare
          (d) bi gefen hanya, banda kalle-kalle, da hira a kan hanya.
       Manzan Allah S.A.W ya bayyana ce wa duk matar da ta fita daga gidanta ta sanya turare don wasu su kanshinsa to ita mazinaciyace
(32) BANDA TSINA GA MIJI
  Rashin kunya tsiwa, gwalewa da yawan tsiya ga mace kan sanya miji yayi watsi da mace, ya ji ba ya kaunarta, kai ganintama baya son yi.
          Don haka amarya ki zama mai tausasasshiya murya, mai kunya wajen Magana. Amma idan kina tare da waninsa kya iya yin maganar dakike so.
      Allah S.A.W yana cewa.
{فلا تخضعن بالقول فيطمع الذى فى قلبه مرض وقلن قولا معروفا} الأحزاب/32
[..Saboda haka kada ,kada ku sassautar da Magana ,har wanda ked a cuta a cikin zuciyarsa ya yi dammani, kuma ku fadi Magana ta alheri]Ahzab/32
(33) KADA KI BAR WANI YA SHIGO GIDANSA SAI DA IZININSA
      Shigar maza barlate cikin gida yana zubarda mutuncin matar gidan da mijinta. Don haka ba ko wanne mutum ne zai shigo gida ba, mutukar ba mijinki ne yabashi izini ba.
      Manzon Allah S,A.W yana cewa:"kada mace tab a da izini a cikin gidansa(mijinta) said a izininsa”bukari da muslim ne suka rawaito.
(34)IDAR DA SAKO GARE SHI
     A duk lokacin da wani ko wata ya kawo wani sako don kibawa mijinki to ki yi kokari ki sauke wannan nauyin idan kuwa kika ki to mutun cinki zai zube a wajan
Bakin mijinki kuma mijin ya ji ba ya kaunarki
 (35)ZAMAN AURE SAI DA ILIMI
Yin aure amarya ba yazamakarshen neman ilimi .kisani wajibi ne gareki ,ki zama mai karawakaki ilimi tahanyar karance- karance da neman ilimin a wajen mijinki.
  Idan ba shi da shi , ko ba shi da lokacin koya miki to sai ki nemi izininsa don ki je ki nema ta hanyar saki a makaranta ko nema maki mai koya miki a gida.
 Nana A'sha R.A. tna cewa " Madalla da matan Ansarawa(mutanen madina) da kunya bat a hana musu su nemi ilimin addini" Muslim ne ya ruwaito.
(36) KI TSAFTACE GIDANKI
 Kada ki yarda mai gidanki ya dawo daga wajen neman abinci ya zo ya tarar da gidanki kaca-kaca, ke ma busu-busu, 'ya'yanki ma haka.Don yin haka zai sanya kyama a tsakaninki da shi, ya rika gudunki, a karshe ya auro maki wata, ko ya bi wata hanyar da aban, kada dai ki manta tsafta cikon addini ce.
(37) KADA KI YI FADA DA MIJINKI A GABAN 'YA'YANKI
      Duk wani abu da ya taso tsakaninki da mijinki, kada ki yarda hankalinki ya bata, har ku yi fada a gaban 'ya'yanki ko kishiyoyinki, ko wasu da ban. Don yin haka kan bata yara, ya zubar da mutunciki kowa ma ya kyamace ki.
(38) BANDA LALUBEN ALJIHUN MIJI
       Wasu makwadaitan mata, mugwaye suna laluben aljihun miji, suna neman kudi ko wani abin. Yin haka ha'inci ne kuma duk son da yake yi miki kararki ki yi, don ba zai zauna da barauniya ba.
(39) KI GUJIYIN KARYA DA GULMA GARESHI
   Daga lokacin da mijinki ya gano ke makaryaciya ce, ba zai taba yarda da ke ba. Wanda hakan kan iya janyo sakinki, da yi miki korar kare.
     Domin karya haramun ce.
(40) TSAFTAR JIKI DA TUFAFI
     Amarya! A kullum ki zama mai kula wa dajikinki da tufafinki, kada ki zauna da dauda, ko a tsakar gida ki zauna kanki a kwance, kin yi daurin karji.
     A kullum ki yi shigar da za ta dauki hankalin mijinki. Idan kika bari yajiki kina wari ko doyi, ba zai taba sha'awarki ba. Don haka ki rika kitso, ki shafa turare, ki yi kunshi , da dai sauran abubuwan da zai sa ki yi fyas abar sha'awa.
(41) BANDA ABOKI A WAJE
  Dabi'ar wasu tsinannun matace, rikar aboki a waje baya ga miji, a wajin aiki, ko makaranta, da makamantan haka. Yin hakan sabawa Allah ne,shiga tsinuwar mala'iku ne, fita daga rahamar Allah ne.
      Kuma kada ki yarda ki fada cikin kungiyar mugwayan kawaye masu madugo ko neman maza, da makamantan haka.
Don yin haka, asara ce, tabawa ce da kuma halaka.
     (42) BANDA HA'INCI A GIDA KO A WAJE
       Amarya ki zama mai rukon amana, mai cika alkawari, a wajen mijinki da sauran jama'a sai ki rabauta. Ki zama daya daga cikin muminan mata, masu shiga Aljanna ba tare da hisabi ba.
 (43) KADA KI MATSAWA MIJINKI WAJAN CIYARWA
    Ciyarwa ta kunshi abinci, tufafi da kuma wurin kwana, kada ki yarda amarya ki dora masa abin da ya fi karfinsa.
   Allah S.W.T. yana cewa:*
  (ma'abocin wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda aka takura masa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah ya ba shi. Allah ba ya dora wa wani rai sai abin da ya ba ta.da sannu Allah zai sanya sauki bayan tsanani). Talaq /7
 (44) NEMI YAFEWARSA IDAN KIN MASA LAIFI
      Matar na tuba ba ta rasa miji. A duk lokacin da mijinki ya ce kin yi masa laifi, ki ba shi hakuri.
       Manzan Allah S.A.W. ya ce: ba na ba ku labari mafi alherin matanku ba a cikin alanna? Muka ce: Eh! (Ba mu mana) Ya ma'aikin Allah ya ce: dukkan wata abar kauna, mai haihuwa (wadda) idan mijinta ya yi fishi sai ta ce: gahannuwana a hanunka bazan yi barci ko rintsawa ba har sai (ka daina fushi)"
(45) KADA KI BOYE MASA LAIFIN DA YA YI MIKI
      Idan mijinki ya yi miki laifi, to ki fito fili kigayamasa, kada ki boye masa, domin shi bai sani ba, a karshe sai ki jib a kya son sa.
(46) TARYAR MIJI DA WALWALA
      Idan mijinki ya dawo, kitarye shi da fara'a, sannan ki dubi fuskarsa don ki gane irin halin da yake cikia wannan lokacin, ki masa maraba da barka da zuwa ki karbi kayan hannunsa, ki karbi hularsa da babbar riga, yi masa shinfida don ya zauna ya huta, kawo masa ruwa, da abinci ,yi masa fifita, da Magana mai dadi, yin haka zai kara son ki, ya rika tunaninki idan ya fita.
(47) ADDU'A GA MIJI
   Ki sani amarya mijinki, kullum ya na bukatar addu'arki, don haka ki yawai ta masa addu'a a duk lokacin da zai fita waje aiki, k ice "A dawo lafiya Allah ya bad a sa'a. idan ki yi salla ki masa addu'a Allah yataimake shi ya arurta sha, da dai makamantan haka. Domin addu'arki karbabbiya ce a kan haka.
(48)BANDA MUMMUNAN KISHI
     Kishi kimallon mata. Idan Allah ya nufeki da shiga wajen kishiyoyi, ko Allah ya hore wa mijinki zai kara aure, kada ki dauki mummunan kishi ki sa a zuciyarki , ki tuna Allah S.W.T ne ya umarci maza da aurar mata bibiyu, ko uku-uku, ko ma hudu.
     Ba zaki san mijin ki adali ba ne,ko kuma yana kaunarki sai ya kawo miki abokiyar zama. Taimaka masa ya zama mai biyayya ga umarnin Allah da yake cewa
{فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثلاث ورباع ، فإن خفتم ألا تعدلوا فواحدة أو ما ملكت أيمانكم} النساء؟3
{Ku auri abin day a yi muku dadi azuciya daga mata, biyu ko uku ko hudu. Idan ba za ku iya adalci ba ( a tsakaninsu) to ku auri daya, ko abin da kuka mallaka ( daga kuyangi)….}Nasa’i/3
(49)KI GUJE WA MASU GULMA DA KINIBIBI
    Akwai mugayan tsofaffi damugayan kawaye da sukan je gidajen amare, ba daniyyar alheri ba. Burinsu su ga sun bata tsakanin miji da mata, ta hanyar munafunci da gulma da kinibibi.
     Irin wadanan masu irin wannan hali ba sa tare da manza Allah S.A.W. yana cewa:
      "Ba ya tar da mu wanda ya bata matar wani mutum"Ahmad ne ya ruwaito J:5, hadis 352
 (50) KADA KI NEMI SAKI
     Aduk wahala, a duk rintsi kada ki nemi mijinki ya sake ki don yin haka babban sabo ne. manza Allah S.A.W yana ce wa: duk matar da ta nemi mijinta ya sake tab a tare da wani laifi ba (na shari'a) to kanshin aljanna ya haramta a gareta.
AKARSHE
     Amarya dukkan nasihohin nan da muka ambata a baya tushensu tsoron Allah,biyayya ga miji , yi na , bari na bari, soyayyar da aka ginata da ikilasi, ake yin ta don Allah, saboda Allah.
     A kullum Allah da Manzansa su zama madubinki a cikin rayuwarki ta aure. Allah ya zama jagora.
ABUBUWAN DA AKA DUBA
(1) Alkur’ani Mai girma.
(2) Bukar Muh’d Ibrahim, Lailatul Zifaf wa shahrul Asal,M.Safa 2005/1423.
(3) Aliyyu Abdul’Ala Al-Tahtani, Kifa Tas’idana Zaujiki. M.Safa 1421/2000
(4) Aliyyuabdul’Ala al-tahtawi,Mafatihu al –Sa’adatuz Zaujiyya, M.Safa 1422/2001
(5) Muh’d Mahmud Abdullah, Kaifa Tas’idina Zaujiki Wa Kaifa Tas’idina Zaujataka,Darul Fajar,1420/1999
(6) Muh’d Sadiqul Manshawi,Fannul Ta’ammul Bainaz Zaujain, Darul Fadilah ,2006/1427
(7) Dr. Muh’d Wasfi, Al-mausu’atul Shamila fi ‘alaqatul Rajul Bil Mar’ah,Darul FAdilah 2006.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top