Wannan makala ce da muka yi bayan da muka bukaci ku aiko tambayoyinku kan Sheikh Dahiru Usman Bauchi. BBC ta tattauna da Sheikh domin bayar da amsar tambayoyin naku.
Shiekh Dahiru Usman Bauchi babban malamin darikar Tijjaniyya ne da ake ji da shi a nahiyar Afirka, sannan malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al'kur'ani, littafin musulmi mafi girma.
Shehun malamin na daya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.

Tarihin sheikh Dahiru Bauchi

Wannan tambaya ce da muka samu daga dumbin mutane da suka hada da Ahmad Muhammad da Wada Muhammad Musa Danmaliki Kumbotso Kano
BBC ta mika wannan tambaya ga Sheikh Dahiru Bauchi ga kuma amsar da ya bayar:
An haifi Sheikh Dahiru ne a ranar 28 ga watan Yunin 1927, dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346.
An haife shi a wani gari da ake kira Nafada da ke jihar Gombe, wanda garin mahaifiyarsa ce, "kasancewar a al'adar Fulani ana haihuwar dan fari ne a gidansu mahaifiyarsa," in ji shi.
Ya kara da cewa: "Ni Bafulatani ne ta wurin uwa da uba. Dukkanin kakannina hudu Fulani ne.
"Sunan mahaifiyata Maryam 'yar Hardo Sulaiman. Sunan Mahaifina Alhaji Usman dan Alhaji Adam."
Sheikh Dahiru ya haddace kur'ani a wurin mahaifinsa kafin daga bisani ya tura shi Bauchi domin neman tilawa.
Mahaifinsa almajirin Shehu Ibrahim Nyass ne kuma mukaddami a cikin darikar Tijjaniyya ta hanyar Amadu Futiy kafin Shehi Ibrahim Nyass ya bayyana.
"Mahaifiyata ita ma ta je Kaulaha har sau biyu, kuma Shehu ya kaddamar da ita har ya ba ta carbi, saboda haka ni da mahaifina da mahaifiyata da 'ya'yana da jikokina duk gaba daya mun taru a cikin Shehu Ibrahim,"
Ya yi auren fari a shekarar 1948 lokacin yana da shekara 20 "da wata daya."

Yawan 'ya'yan Shehu

Tambaya ce da muka samu daga Murtala Shu'aibu Gama
Sheikh Dahiru ya ce yana da 'ya'ya kimanin 80 kuma 70 daga cikinsu sun haddace alkur'ani.
"Wasu daga cikin yarana sun haddace kur'ani tun suna shekara bakwai da haihuwa kuma tun ma kafin su iya rubutu a allo.
"Akwai yarana hudu da suka haddace kur'ani a shekara biyar kamar daya daga cikin 'ya'yana da ke Kaduna. Su da ka suke haddacewa amma dai ba zai hana su rubutu a allo ba idan suka girma.
"Sai dai ban sani ba ko a cikin 'ya'yan nawa akwai wanda ya rubuta kur'ani saboda su kan fita kasashen waje domin neman karatu na sauran fannonin addini da ma boko.
"Yanzu ma akwai daktoci a cikin yaran," a cewar Shehun Malamin.
Matan Shehi nawa?
Mun sami wannan tambayar ne daga Usman Sale Jimeta da Salisu Garba Warure.
BBC kuma ta mika tambayar ga daya daga cikin 'ya'yan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda ya bayar da amsa kamar haka:
"Matan Shehi hudu ne a yanzu haka. Sai dai kuma da dama sun mutu sannan kuma wasu da dama sun fita."
A ina ya Shehi ya yi karatu?
Tambaya ce da muka samu daga mutane da dama amma da yawansu ba su fadi sunayensu ba.
Sheikh Dahiru ya ce ya haddace kur'ani a hannun mahaifinsa Alhaji Usman dan Alhaji Adam ne domin shi ma mahaddacin alkur'ani ne.
Daga nan ne ya tura shi wurin malamai da dama domin tilawa, "kuma Alhamdulillahi na kan ji mutane na karin gishiri suna kira na gwani," in ji Malam.
Malam ya je Bauchi domin karatu. Malaman da ya yi karatu a hannunsu sun hada da Malam Ahmadu na Sabon gari da Gwani dan Fika da malam Alhaji na Gombe da dai sauran su.
Ya kara da cewa: "Ba gaskiya ba ne cewa na yi karatu wurin Shehi Nasiru Kabara. Malam Abubakar Gumi ne ya yi karatu wurin Shehi Nasiru Kabara.
"Na kuma karbi darikar Tijjaniya a hannun mahaifina."
Sheikh Dahiru Bauchi
Iyalansa
Rayuwar Dahiru Bauchi a takaice
Shekararsa 92
  • 80Yawan 'ya'yansa
  • 70'Ya'yansa mahaddatan kur'ani
  • 48Yawan aikin hajjinsa
  • 300Yawan makarantunsa
  • 1948Shekarar da ya yi aure
  • 1927Shekarar da aka haife shi
Bayanai: Daga bakinsa
Ko Shehi ya rubuta Alkur'ani?
Sheikh Dahiru Bauchi ya bayar da amsa kamar haka:
"Bayan na haddace Alkur'ani inda ake kira na gwani ko gangaran, na rubuta Alkur'ani na farko na bai wa babana kuma malamina kyauta.
"Na kuma rubuta na biyu wasu sun manta. Na fara rubuta na uku amma ban gama ba har yanzu.
"Ina da matsalar agana a idanuna dalilin da ya sa ba ni da nishadi kan duk abin da za a kalla," a cewarsa.
Malamin ya ce matsalar idanun ce ta sa bai yi wasu rubuce-rubuce ba a fannoni.
Dangane kuma da tafsirin Alkur'ani, ya ce ya fara ne a shekarar 1951 ko 1952.
"Ni kuma tafsirina ba na duba takarda saboda haka Annabi yake yi, sannan haka ma manyan bayin Allah suka yi.
"Idan mutane suka tambaye ni me ya sa ba na rike takarda a tafsirina, sai na tambaye su cewa kuna rike kur'ani idan kuna karanta Suratul Ikhlas a sallah.
"Na san kur'ani saboda haka ba sai na rike shi ba idan zan yi tafisiri," in ji Sheikh.
Sheikh na addu'a
Iyalansa
Idan mutane suka tambaye ni me ya sa ba na rike takarda a tafsirina, sai na tambaye su cewa kuna rike kur'ani idan kuna karanta Suratul Ikhlas a sallah?
Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Bayani daga bakinsa

Mene ne sirrin karatun Shehi da yaransa?

Shehun Malamin ya ce: "Sirri na Allah ne. Da farko dai muna kiran wani abu da ake kira fafau da muke rubuta wa mutum ya sha domin zuciyarsa ta fafe ya haddace kur'ani.
"Muna da wani sirri da muke rubuta wa yaro a duk Laraba sau uku. Ana rubuta masa ya lashe. Zai haddace kur'ani kuma duk garin da ya zauna sai an yi tafiyar wata uku kafin a samu mahaddaci kamarsa.
"Sai dai ba mu sani ba ko wata ukun na tafiyar kafa ne ko kuma a mota," kamar yadda ya ce.
Ya ce ada can sai sun je garin Barebari sannan su haddace kur'ani amma yanzu ko ina ana iya haddace shi.
Suna da makarantu kusan 300 na almajirai a Najeriya, kuma yaran ba sa wuce shekaru hudu ba tare da sun haddace kur'ani ba sai dai idan suna da nauyin kwakwalwa.

Sau nawa Sheikh ya yi aikin hajji?

Sheikh Dahiru Bauchi ya ba da amsa kamar haka;
Tun daga shekarar 1970 kawo yau sau daya ne kawai bai je aikin Hajji ba.
Hakan na nufin ya yi aikin hajji sau 48.

Yare nawa Shehi yake ji?

Ita ma wannan tambayar mun same ta daga mutane da dama
"Ni dai Bafulatani ne kuma ko an ji ni ina Fulatanci babu mamaki. Mahaifina yana da tsangaya a kasar Borno inda yake da almajirai Hausawa da Barebari.
"Saboda haka tun a lokacin na iya Hausa da Barbarci kuma tun ina karami na tashi da wadannan.
"Da na girma kuma na iya Larabci kadan da yaren Wolof na su Shehi Nyass da Bolanci.


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top