Mai rike da kambun kungiyar kwallon kafan Nijeriya, Ahmed Musa, ya nuna godiyarshi ga shuwagabannin ‘yan wasa a kan yadda suke mishi in yana azumi.
Amma yace, babu abinda zai hana shi azumin shi tunda ibada ne, kuma ba ya hana shi harkokin shi.
“Tun ina karamin yaro nake azumi. Bana tunanin zan iya daina azumin, saboda na zama kwararren dan wasan kwallon kafa. Na yi wasanni da yawa tare da horarwa kuma duk a cikin watan Ramadan, kuma babu abinda hakan ya canza.”
“A matsayin dan wasan kwallon kafa kuma musulmi, ba ni da wani dalili na kin yin azumin watan Ramadan.
An amince mana da kada mu yi azumi ne idan muna kan hanyar doguwar tafiya, a kalla wacce zata dau sa’o’I hudu zuwa biyar.”
“Da yawan shugabannin ‘yan wasa wadanda ba musulmai ba kan tausaya min. Suna mamakin yadda nake iya wasa bayan ina azumi. Amma addinina ne kuma babu abinda zai hanani yin shi. Dole ne in mutunta addinina,” Musa ya sanar da Opera News.
Musa ya yi azumi a lokacin gasar kofin duniya na shekarar 2014 da 2018, kuma duk ya yi nasarar wurga kwallo cikin raga a dukkan wasannin.
©HausaLoaded
Post a Comment