Duk A Cikin Shirin 'Yan Fim da Finafinai, Wanda Jaridar Dimokuradiyya Ke Daukar Nauyi

Wakilinmu Mukhtar Yakubu Kano

Daya daga cikin jarumai masu tasowa a cikin masana'antar finafinai ta kannywood. Ummi El Abdul wadda aka fi sani da Ummi Duniyar nan ta bayyana harkar fim a matsayin wata harka ta sana'a da neman rufin asiri ga masu yin ta don haka kuma ba wata harka ba ce da ta ke hana aure musamman ga Mata da su ke yin harkar.

Jarumar ta bayyana haka ne ga wakilin mu Mukhtar Yakubu, a lokacin da su ke tattaunawa dangane da kallon da ake yi musa kuma ana cewa duk wadda ta shiga harkar fim ta kan jingine maganar aure ne kawai ta mike kafa ta yi duk abin da ta ke so, in da Jarumar ta fara bada amsa da cewar.

"Kawai ina ganin fassara ce ta mutane wadanda ba su da masaniya a kan al'marin Amma ai komai dadin da ki ke ji, saboda hankalin iyayen ki ya kwanta ke ma za ki so kiyi auren Sai dai  in da ma can mace ba ta da niyya".

Mun tambaye ta dangane da masu ra'ayin cewa, bai kamata ba a ce 'yar fim ta yi aure, ta fito kuma a kara ba ta wata dama ta ci gaba da yin fim.

Sai ta ce "Ai abin da mutane ba su sani ba shi ne ko da yarinya ta yi aure, saboda rashin fahimtar da mutane ba sa yi mana ba, Sai ki ga iyaye da dangin mijin ki sun sa ki a gaba, har Sai sun ga bayan auren.

To ni ina ganin don an saki 'yar fim ta dawo fim ba wani abu ba ne, domin wata idan ba a saka ta ba Sai ta kama wata hanya mai hadari, to ka ga ai babu dadi. "

Dagakarshe Ummi ta yi kira ga jama'a da su rinka yi musu uziri, domin kuwa su ma' yan fim mutane ne kamar yadda sauran mutane su ke, za su iya yin daidai, kuma za su iya yin kuskure.

Hakkin Mallaka, Jaridar Dimokuradiyya

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top