Daya daga cikin manyan daraktocin Kannywood wanda su ka dade su na daukar nauyin  manyan fina-finai tare da ba da umarni, Darakta Hafizu Bello ya bayyana wasu shirye-shiryen da su ke yi na daga  darajar masana'antar Kannywood tare da fito da hanyoyin da zai kaita ga wani matakin da ba a ta tsammani ba.

Daraktan ya fara da cewa shi mutun ne mai kulawa da aikin shi,  kuma yana kokarin ya ga ya kare sana'ar shi ta hanyar da ba za'a raina ta ba. Ya kuma kara da cewa ba ya yarda ko da wasa a ce za a mai maita wani fim da ya bada umarni a baya tunda yasan ya yi aiki mai kyau kuma fim ya na tafiya ne da zamani, ana maimaita fim ne idan akwai Karancin labarai kuma ba wai babu ba ne, akwai labarai da yawa wanda idan aka dauke su zasu kayatar sosai.

“Nan da wasu shekaru kadan kannywood za ta kai wani matakin da kowa sai ya  sha mamakinta, dalilin fadin hakan shi ne akwai wasu  manyan fina-finan najeriya guda biyu wanda su ka yi fice a nahiyar Afirka tare da tara manya kudaden shiga masu suna  Joy da kuma Lion Heart, amma duk da wanna ficen nasu an kori fina-finan daga shiga gasar fina-finai ta duniya saboda ana ganin ba su kai su shiga gasar ba.

Yin haka ya na nuna cewa ke nan ya kamata a Kara inganta fina-finai a Afirka ba ki daya domin yin hakan  zai kara saka abubuwa su daidaita. Mutum ya tsaya ya yi fim mai kyau, kuma gyaran ya shafi ko wanne bangare; hausa, Igbo, da yoruba, yin fina-finai ingantattu shine zai sa a iya dora su a manya kafafen yanar gizo irinsu Northflix da sauransu”. Inji Daraktan

Wakilin mu ya tambaye shi, ko wane irin gyararraki yake tunanin zasu kawo akan lalacewar kasuwar fim?

“Gyara ai ana kan samu tun da har ana kai finafinai sinima kuma su karbu, ana kokarin dawo da al’adar da ta haska finafinai a gidajen sinima wanda dama can akwai su kafin a sake su a kasuwa, zuwan  talabijin ya sa mutane suka guji wannan al’adar.

Kuma an fara samun nasara tunda jama’a sun fara karbar canjin ko da anyi fim yanzu an daina buga shi a fefen CD dole sai dai a kai sinima da gidajen talabijin, tunda  zamanin ya koma na yanar gizo da sauransu wanda nan yakamata ace an fi maida hankali akai yanzu don samar da abinda ake so, tunda wancan ya riga da ya wuce kuma bazai dawo ba”. A cewar Hafizu

Wace shawara zaka ba jaruman Kannywood a kan yawan fadace fadacen da su ke yi?

“To fada a masana'anta irin wannan ai abu wanda ya zama ruwan dare ne, ba wani abu bane tunda duk masana'antun finafinai na duniya ana samun wannan matsalar, amma shawara daya da nake ganin zan bada ita ce gaba daya masana’antar kannywood a tashi a nemi ilimi, in akwai cikakken ilimi to ko za a yi rigimar ma baza ta dinga daukar  zafi haka ba. Kuma idan nace ilimi to ina nufin ilimin ita kanta sana’ar fim din ba wai ilimi na degree ko wani abu ba. Ina ganin idan aka samu ilimin sana’ar fim to za a samu maslaha kuma ce-ce-ku-ce zai ragu “ inji Darakta Hafizu Bello.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top