TSOTSON FARJIN MACE A LOKACIN SADUWA – DR JAMILU ZAREWA

TSOTSON FARJIN MACE YAYIN SADUWA ! !

Tambaya :

Assalamu alaikum, M. Na kasance ina tsotsan azzakarin mijina, shi kuma yana wasa da gabana da harshensa kafin mu sadu, ina matsayin haka a addinin musulunci.

Amsa :

To ‘yar’uwa hakan ya halatta, ba matsala a sharian ce, saboda an rawaito halaccin haka, daga magabata, daga cikinsu akwai Imamu Malik, saidai ya wajaba a tabbatar an tsaftace wurin musamman farjin mata, saboda a bude yake, sannan kuma wuri ne da ake yin haila, ake kuma zuba maniyyi, ga shi kuma yana kusa da wajan yin

bahaya, wasu masana likitanci suna bada shawarar cewa : a dinga wanke wurin da gishiri kafin a tsotsa, saboda neman kariya.

Allah madaukakin sarki a cikin suratul Bakara aya ta : 223, ya kwatanta mace ga mijinta da gona, wannan sai ya nuna dukkan bangarorin jikinta ya halatta a ji dadi da su, in ban da cikin dubura wacce nassi ya togace.

Allah ne mafi sani.

Duba : Mawahibul-jalil sharhin Muktasarul Khalil 3\406

Daga :-darulfatawa

ku duba asalin wannan posting din daga babban shafin mu TSOTSON FARJIN MACE A LOKACIN SADUWA – DR JAMILU ZAREWA mun dauko wannan posting din daga babban shafin mu wato ArewaFresh.com.


©Arewafresh

Post a Comment

 
Top