Ci gaba daga makon jiya

3. Mai Juna-biyu (Mai ciki), Galibin mata masu juna biyu basa al’ada, sabo da haka da zarar mace tana da juna biyu (ciki) sai kuma ta ga al’ada to kada ta yi sakaci wurin tuntubar likita. Idan al’ada ta zowa mace mai juna biyu to ida cikin ya kai watanni uku zuwa biyar zata iya yin al’ada ta kwanaki sha-biyar zuwa ashirin, idan kuma cikin ya kai watanni shida to al’adar zata iya daukar kwanaki ashirin zuwa ashirin da biyar, kada a sha’afa wurin tuntubar likita idan ana da juna biyu kuma aka ga jini.

Idan mace jini yana mata wasa wato ya zo yau gobe sai kuma ya dauke bayan kwanaki uku sai kuma ya dawo to abinda zata yi anan shine, ta tsaya ta yi karatun ta natsu, sai ta lissafa kwanakin da jinin ya zo sune kwanakin al’ada sai kuma ta ware kwanakin da jinin bai zoba sune kwanakin tsarki domin da hakane zata cika kwanakinta na al’ada, misali kwanaki tara sai ya zo a rana ta farko da ta biyu sai bai zoba a rana ta uku da ta hudu sai ya zo rana ta biyar amma bai zo ba a ta shida da ta bakwai sai ya zo a ta takwas da ta tara. To anan sai muce ta yi al’adar kwana biyar a cikin kwanaki goma, wannan matar ita ake kira (Al-Mulaffika) alarabcin mata masu al’ada. Idan ya zama an sami tazarar kwanaki takwas ko sha-biyar tsakanin daukewarsa da dawowarsa to na biyun zai zama sabon jinine kenan, ba na da bane ya dawa.

Alamar Daukewar Jinin Al’ada, idan jinin al’ada ya dauke akwai alama da shara’a ta sanya domin ya zama shine manuniya akan cewar al’adarki ta dauke, wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka.

1.Bushewar Gaba: Abinda ake nufi anan shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da shi busasshe ba wani jini a tare da shi, to da zarar ta ga haka to ta tabbata al’adarta ta dauke.

2.Farar Kumfa: wannan wani ruwane fari mai laushi da yake zuwa karshan al’ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al’adarta to ta sani ta kammala. Wadannan alamomi su suke nuna daukewar al’adar mace, idan mace bata taba ganin al’adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai-tsaye ta samu tsarki ba sai ta jira farar kumfaba, amma idan wacce ta saba ganice sai ta ga bushewar gaba to malamai sukace zata dan saurara kadan domin jirar faran kumfa, amma jinkirin ba zai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba.

A dunkule dai kowanne daya daga cikin wadannan abubuwa guda biyu yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu alokaci gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai ta yi wankan tsarki domin ta ci gaba da ibada, domin idan bata yi wanka ba ko da jinin ya dauke mijinta ba zai sadu da itaba ba kuma zata ba za tayi sallaba, da dai sauransu. Idan mace ta ga ruwa fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin al’ada to kada ta damu ta ci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma idan a karshen jinine to wannan ba komai, Ummu Atiyyah mai dakin ma’aikin Allah (S) tace, “Mun kasance bama lissafa (Ruwa) fatsi-fatsi da diddiga-diddiga bayan tsarki da cewa wani abune”. Abu Daud Hadisi Na: 307, Nasa’i, Hadisi Na: 368, Ibnu Majah Hadisi Na: 647, Darimi Hadisi Na: 865.

Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba’ace tata shi cikin dare ba domin ta duba. Idan mai al’ada ko mai biki (jinin haihuwa) ta ga tsarki kafin rana ta fadi to sallar azahar da la’asar sun hau kanta, hakanan kuma idan ta ga tsarki kafin hudowar alfiji to tabbas za ta yi sallar magariba da Isha.

Abubuwan da basu halatta ga mai-al’adaba, anan za’a lissafa abubuwan da basu halatta mai al’ada ta yi su ba ko ayi mata ba, wadannan abubuwane guda goma.


1.Sallah, Bai halatta mai al’ada ta yi salla ba farilla ko nafila, idan kuma tayi ma ba’a karba ba, sannan kuma ta yi laifi, sannan bayan ta kammala al’adar ba zata rama sallolinba.

2.Saki, Baya halatta matar da take al’ada a saketa, wannan ya sabawa karantarwar musulunci, saboda haka koda yana son ya saketa to ya bari sai ta kammala al’ada kafin ya sadu da ita sai ya saketa, amma idan ya saketa tana jinin al’adar to sakin ya yi amma za’a tilasta shi ya mayar da ita idan sakin bai kai uku ba.

3.Dawafi, Bai halatta mai al’ada ta yi dawafin Ka’abah, amma zata yi sauran dukkan abinda maniyyaci yake yi, kamar tsaiwar Arafah da kwanan mina dana muzdalifa da jifa da Labbaika, da daidai sauransu.

4.Zama A Masallaci, mai al’adah ba zata zauna a cikin masallaciba, domin sauraron karatu ko karantarwa ko taro da dai sauransu.

5.Azumi, Bai halatta mai al’ada ta yi azumi na farilla ko na nafila, idan ta yi kuma bai yiba, saboda haka zata lissafa azumin da ta sha bayan watan ya wuce sai ta ramasu. Ba’a ajiye azumi domin tsammanin gobe al’ada zata zo, amma dazaran ta zo ba azumi a kanta, idan ba ta zo ba azumi Yana kanta, ko da kin ji tafiyar jinin ajiki amma bai fitoba to biki fara al’ada ba, sai ya fitane za’a fara lissafi.

6.Taba Alkur’ani, mai al’ada bata taba kasantuwarsa littafi mai tsarki sannan kuma ita bata da tsarki, amma wannan baya hana idan ta ganshi zai fadi ta daukeshi ta gyara masa wuri.

7.Karatun Alkur’ani, mai al’ada bata karanta Alkur’ani, duk da cewa wadansu malamai suna ganin ya halatta ta karantashi, domin kada ta manta sabanin dauka.
8.Saduwa, Bai halatta ba saduwa da mace tana al’ada, idan ta ki yadda da mijinta ya sadu da ita domin tana al’ada ba za’ace ta sabawa Allah ba bihasalima ta yi biyayyane ga mijin, bai halatta a sadu da mace tana al’adaba har sai al’adar ta dauke kuma ta yi wankan tsarki, kenan koda al’adar ta dauke amma ba tayi wanka ba to bai halatta a sadu da ita ba. Ya halatta miji ya taba duk inda yake so a jikin matarsa alokacin da take al’ada bayan ta yi kunzugu in ban da daga cibiyarta zuwa gwiwarta wannan kan bai halattaba har sai jinin ya dauke kuma tayi wanka, haka nan itama ya halatta ta taba ko ina a jikinsa duk da tana al’ada.

9.Tabbatar Da Rashin Tsarki, Al’ada tana tabbatar da wacce take da ita bata da tsarki.

10.Wajabta Wanka, Al’ada tana wajabta wanka, wato dukkan matar da ta yi al’ada kuma al’adar ta dauke to wankan tsarki ya wajaba akanta. Shi kuma bayani akan abinda ya shafi wankan tsarki zamu yi a nan gaba. 

Daga wadannan bayanan da suka gabata ya bayyana a fili cewa lalle jinin al’ada bakaramin hukunce-hukunce yake da shi ba, kuma lalle idan aka kallaci yadda ake sakaci tsakanin maza da mata akan abinda ya shafi wannan al’amari to lalle abin yana da ban tsoro.



© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top