A mafi yawan lokuta mutane kan yi fama da cutar tari da mura da hakan kan iya zafi ya zama har sai ya kwantar da mutum.

Bisa ga bayyanan da Wani likita dake asibitin jami’ar Rush a Chicago, kasar Amurka Mark Yoder ya nuna cewa tari ko mura cutuka ne da ake iya kamuwa da su idan kwayar cutar da ake kira ‘Virus’ ta kama mutum.

Ya ce kwayar ‘Virus’ na iya kama mutum ne idan ana yawan mu’amula da abubuwa masu sanyi.

” idan sanyi ta kama jikin mutum ne ake kamuwa da mura sannan idan ya kama hakarkari sai kaga an fara tari.”

Ya kuma kara da cewa wannan kwayar cuta na da wuyan magani don haka ya sa idan mutum ya kamu da ita dole ya kaurace wa duk hanyoyin da sanyi zai iya kama jikin sa.

Yadda za ka kare kanka

1. Shan ruwa: Shan ruwa na da mahimmanci sosai saboda yana mayar wa jikin ruwan da ya rasa saboda kamuwa daya yi da cutar. Mutum na rasa ruwan jikin sa idan ya kamu da cutar ta hanyar yawan fitar da majina da yawu sannan kuma saboda tari da ake yi makogoro zai yi ta bushewa.

2. Shan shayi mai zafi musamman wanda aka hada ta da kayan kanshi kamar su cita, kanimfari, masoro sannan ana iya hadawa da zuma.

3. Yin wanka da ruwan dumi da kuma yin surace na taimaka wajen kawar da mura.

4. A hakura da yin amfani da turare masu kanshi da karfi musamman turaren wuta.

5. A Gujewa kura, shakar hayakin taba da kuma zukan ta da shakar hayakin mota ko kuma na janareta na.

6. A daina shan ruwan sanyi.

7. Shan maganin mura kamar yadda likita ya fadi.

SHARE.


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top