Wani mazaunin garin mai suna Aminu ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace hakan ya faru a farkon makon nan yayin wata ziyara da Sanatan ya kai garin Kankiya, inda aka samu wani matashi ya zazzageshi, shi kuma ya ga ba zai jure bay a cakumo yaron ya yi ta dukansa, yaron ma yana ramawa.
Majiyar Legit.ng ta bayyana musabbabin wannan rikici shine: “A lokacin da ake yakin neman zaben Sanatan na farko a shekarar data gabata wasu matasa suka samu hatsari, har wasunsu suka karairaye, amma duk alkawarin da Sanatan ya yi musu bai cika musu ba.
“Daga cikin alkawarin har da alkawarin saya musu babura, amma ya yi watsi dasu bayan ya cimma bukatarsa, illa N50,000 daya basu, shi ne da yazo yaran suka yi masa rashin kunya, aka samu guda daga cikinsu ya fito fili yana zaginsa a gabansa.
“Bayan sun gama dambe da Sanatan sai kuma ya umarci Yansanda su kama yaron, su kuma matasan suka ce sai dai a mutu, ba zasu taba yarda a tafi da abokinsu ba.” Inji shi.
Sai dai Malam Aminu ya bayyana cewa wannan abin daya faru tamkar kaikayi ne ya koma kan mashekiya, sakamakon haka yaran Sanatan suka yi ma wani tsohon dan takarar gwamnan jahar Katsina ihu a ranar zabensa.
©HausaLoaded
Post a Comment