Diyyar naira tiriliyan 3.2 da kotun London ta kakaba wa Najeriya za ta shafi duk wani dan Najeriya, domin kowa sai ya ji a jikin sa.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed.

Gwamnatin Najeriya ta koka matuka yadda biyan diyyar zai iya shafar arziki da tattalin arzikin ta.

Idan har Najeriya ba ta yi nasara wajen daukaka kara ba, to za a kwace kudaden kasar ne ko wasu dukiyoyi da suka shafi kadarorin kasar da ke Birtaniya ko Amurka.

Najeriya ta ce ba ta amince da biyan diyyar ba, saboda tun farko akwai mishkila wajen yadda ta kulla kwangilar aikin gas da kamfanin Birtaniya mai suna P&ID.

Najeriya ta fadi wannan matsayar ta ce a wani taron hadin-guiwa da manema labarai da ministoci uku suka kira ‘yan jarida a Abuja.

Ministocin sun hada da Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed da kuma Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed.

“Wannan hukuncin diyya da aka kakaba wa kasar nan kokari ne kawai aka yi domin a biya wa wani kamfani bukatar sa. Saboda cin fuska ne da kuma zalunci ga kowane dan Najeriya.” Haka Minista Zainab ta furta.

“Mu na ta kokari ta hanyar Ma’aikatar Shari’a domin ganin cewa kotu ta jingine hukuncin biyan diyyar. Domin idan har ba a jingine shi ba, to fa kowane dan Najeriya zai ji jiki.” Cewar Zainab.

An dai yanke wannan hukunci ne makonni biyu da suka gabata a London, inda kotu ta hukunta cewa Najeriya ta biya P&ID dala bilyan 8.9, kwatankwacin naira tiriliyan 3.2.

A taron da suka yi a yau Talata da manema labarai, Ministan Shari’a Malami ya ce tun can farko akwai mishkila wajen yadda aka cimma yarjejeniyar amincewa da kwangilar.

“Dama tun tashin farko an tsara yarjejeniyar kwangilar don a samu mishkila kawai. Idan ba haka ba, ta yaya za a cimma yarjejeniya tsakanin P&ID da kuma Ma’aikatar Albarkatun Mai Fetur Ta Kasa, su biyu kawai? Ita dai wannan ma’aikata ba ta samar da gas, kuma ba a shigar da NNPC a cikin yarjejeniyar ba, ko wasu manyan kamfanonin mai na kasashen waje. Dama an shirya kwangilar don a samu matsala kawai.”

Malami ya ce ciniki ne aka yi, amma cinikin-biri-a-sama, domin ta yaya za a sa hannun samar da abin da ba ku da

“Shi ya sa mu ke ganin akwai bukatar yin kwalkwaran binciken gano yadda aka yi kutinguila da makirci da harkallar shirya wannan kwangila domin gano masu hannu a ciki.

“An shirya kwangilar ce tun farko da nufin dama ba za a yi nasara ba, don kawai a janyo wa Najeriya asara.

A wurin taro da manema labarai din dai har da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile.

Kafin a tashi taron, Zainab ta ci gaba da cewa ikirarin da kamfanin P&ID ya yi cewa ya kashe dala milyan 40 duk shafa-labari-shuni ne.

Daga nan sai ta kalubalanci P&ID su zo Najeriya su nuna inda da kuma yadda zuka kashe dala milyan 40 din da suka yi ikirarin sun kashe a cikin bayani da suka shigar da kara a koun London.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top