Mai girma Ministan sadarwan Najeriya, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami FNCS, FBCS, FIIM ya umarci hukumar NCC ta duba yadda ake zaftarewa mutane kundin hawa yanar gizo watau ‘Data’.

Isa Ali Ibrahim Pantami wanda shi ne rike da kujerar Ministan sadarwa a yanzu ya nemi shugabancin hukumar NCC mai kula da sadarwa a kasar ta binciki kamfanonin da ke aiki a Najeriya.

Ministan ya bukaci a binciki kukan da mutanen Najeriya su ka dade su na yi na cewa kundin hawa yanar gizo da kamfanonin sadarwa ke saidawa, su na karewa da wuri a dalilin zaftare su da ake yi.
Source : Legit
Dr. Pantami ya bada umarni ga hukumar NCC ta yi bincike game da wannan zargi tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin sabawa ka’ida. An dade ana kukan cewa kamfanoni na cutar mutane.


Ministan duk a yau, 29 ga Watan Agusta, 2019, ya kuma bayyana cewa ma’aikatan da ke karkashin za su yi aiki tukuru domin cika alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka.

Dr. Isa Pantami yayi wannan jawabi ne bayan Farfesa Umar Garba Danbatta da sauran mayan NCC su ka kai masa ziyara. Ministan ya ce za a ba rabawa aiki sannan kuma a rika bi ana awo.

Kamfanonin sadarwan da ke aiki a Najeriya sun hada da MTN, Glo, Airtel da 9mobile. Jama’a na kukan cewa ana saida kundin data da ‘dan karen tsada sannan kuma su kan kare da wuri.

Dazu gwamnan Jihar Oyo ya fito gaban Duniya ya bayyana adadin albashinsa. Gwamnan da ya mallaki Biliyan 48 ya ce albashinsa bai kai yadda ya sa rai ba bayan ya karbi N650, 000 kacal.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top