Daga Aliyu Ahmad
A daren ranar Litinin din da ta gabata ne matashiyar jarumar finafinan Hausa, Maryam Ahmed wadda aka fi sani da Maryam K.K ta gamu da tsautsayi, inda ta fada hannun masu garkuwa da mutane a cikin garin Abuja.
A yayin da RARIYA ta yi tattaki zuwa gidansu Maryam dake unguwar Calvary Road a garin Mararrabar Abuja a daren yau, hazikar jarumar mai tasowa, ta bayyana yadda lamarin ya auku, inda ta soma da cewa "bayan mun gama aiki ne da su Darakta Sunusi Oscar, sai na zo titin gefen tashar Jabi dake Abuja zan hau mota zuwa Mararraba/Nyaya.
"A lokacin da na shiga motar ni kadai ce, sai wani ma ya zo ya shiga sai kuma wani a kujerar gaba, daga nan sai muka soma tafiya duk da cewar motar ba ta cika ba. Bayan mun dauki hanya sai na ga sun canza hanya, amma kuma na gagara yin magana. Daga bisani kawai sai na ji an shake min wuya tare da daure min fuska.
"Sai suka karbe wayata da katin ATM dina guda biyu (dayan katin na yayana ne), suka duba kudin dake asusun ajiyata ta banki, sai kuma suka soma kiran lambobin dake cikin wayata suna cewa ga halin da nake ciki don haka a turo musu da kudi ta asusun ajiyar tawa. Wanda hakan ya sa aka yi ta tura musu da kudi".
Maryam ta ci gaba da cewa daga bisani kawai sai ta tsinci kanta a wani kango, inda ta tarar da 'yan mata da dama da wadannan matasan suka yi garkuwa da su. Kuma wadanda aka yi garkuwa da su din dukka mata ne, babu namiji ko daya.
"Ni sun ma tausaya min saboda ba su azabtar da ni sosai ba, amma sauran matan suna shan azaba, akwai wadda ma sun gaban yin cinikin gabanta da nonuwanta za su sayarwa da matsafa", cewar Maryam.
K.K ta kara da cewa masu garkuwa da mutanen sun yi ikrarin cewa su dalibai ne kuma suna yin harkar garkuwar ne domin samun biyan kudin makaranta.
Jarumar ta kara da cewa daga bisani, bayan sun kwace mata wayoyi da kudaden dake hannunta da na cikin asusun ajiyar ta da jakan kayan kwalliyarta na sama da dubu dari, sai suka dauko ta suka watsar a yankin Arae 1 dake cikin Abuja.
©HausaLoaded
Post a Comment