AUREN KASHE WUTA: Ta Kashe Mijinta Domin Ta Koma Gidan Tsohon Mijinta

Matar wadda ta hada kai da wasu maza biyu masu suna Garba Hassan da Sahabi Garba, suna zaune ne a Sabon Gari dake gundumar Illo a karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi.

Majiyarmu ta samu daga facebook shafin rariya,Matar ta kashe mijin nata mai suna Abdullahi Shaho ne domin ta sake auren tsohon mijinta mai suna Idris Garba kamar, yadda shugaban ‘yan sandan jihar Kebbi Muhammad Danjuma ya bayyana.

Shugaban ‘yan sandan ya kara da cewa, za a gurfanar da matar da mazan biyu a gaban kotu domin su fuskanci hukuncin abinda suka aikata.

ku duba asalin wannan posting din daga babban shafin mu AUREN KASHE WUTA: Ta Kashe Mijinta Domin Ta Koma Gidan Tsohon Mijinta mun dauko wannan posting din daga babban shafin mu wato ArewaFresh.com.


©Arewafresh

Post a Comment

 
Top