Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon wadda kuma ta shahara wajan bayar da taimako ga marasa galihu ta taimaki tsohonnan da hotunanshi suka watsu sosai a shafukan sada zumunta bayan da ruwa ya rabashi da muhallinshi.

Taimakon da Hadiza Gabon ta wa Abba Babuga dake Fataskum jihar Yobe shine sake gina mai gidanshi da ruwa ya cinye.

Shafin gidauniyar Hadiza Gabon din na Instagram ya wallafa hotunan yanda tuni aka fara aikin sake ginawa Abba Babuga gidanshi da ruwa ya cinye.

Muna fatan Allah ya saka mata da Alheri


©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top