By NASIR S GWANGWAZO

Fim din Barazana ya bai wa wadanda su ka shiga kallo sa mamaki a sinimar Film House da ke Kano, inda ya zarce yawancin finafinan da a ka saba kalla a sinimar kyau da jan hankali.
Wasu daga cikin masu kallo da LEADERSHIP A YAU ta nemi jin ra’ayinsu kan fim din sun bayyana wa wakilinta cewa, finafinai irin Barazana shi ne ya fi dacewa da kallon sinima, domin fim ne na matasa wanda tabo batutuwan da su ka fi damun su.
“Babban abinda ya fi ba ni sha’awa da fim din Barazana shi ne, batun garkuwa da mutane da a ka tabo, wanda shi ne abinda ya fi damun arewacin Najeriya a yanzu. Dubi yadda yarinya budurwa ta zama abar tausayi saboda raba ta da iyayenta da danginta da kawayenta da a ka yi, a ka killace ta a wani kungurmin daji,” in ji wani dan kallo mai suna Balarabe Habib daga Rijiyar Lemo.

Ita kuwa wata budurwa ’yar kallo da mu ka nemi jin ta bakinta mai suna Sahiba Anwar cewa ta yi, “kafin na shiga kallon fim din Barazana ban yi zaton zai birge ni ba, saboda sai na dauka fim din maza ne kawai na fadace-fadace. Ashe ba haka ba ne. Da na gama kallon fim din kasa tashi na yi. Ashe hawaye ne ya ke fitowa daga idona, saboda tausayin mutuwar da a ka yi a karshen fim din.
“Shi kansa Brown sai da ya ba ni tausayi, duk da cewa shi ne jagoran ’yan garkuwa da mutanen, saboda ya na da imani, bai yarda a yiwa mace fyade ba. Gaskiya Barazana ya birge ni. Ba karya!”
Shi ma wani magidanci wanda ya ce sunansa Alhaji Sambo Iyatu, wanda ya zo kallon fim din tare da iyalinsa, ya shaida wa wakilinmu cewa, “wannan fim din babban darasi ne ga gwamnati da manyan attajirai wajen samar da aikin yi ga matasa, domin rashin aikin yi ya na da alaka da rashin tsaro a kasa.
“Haka nan kuma rundunar ’yan sandan Kano dole ne a yaba ma ta kan yadda ta taimaka fim din nan ya yiwu ba tare da irin hauragiya da kurakurai da mu ka saba gani a wasu finafinan ba. Kuma fim din ya nuna cewa, jami’an tsaro su na shan wahala wajen gudanar da aikinsu, saboda irin sadaukar da rayukansu da su ke yi, don mu ’yan kasa

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top