By HAMZA DAWAKI - 
   

Wayewa, a takaice, ita ce wani yanayi da yakan sauya dabi’ar mutum ta hanyar kara samun haske a lammuran rayuwarsa. Shi ya sa idan ka ji ana cewa “Ai wayayyen mutum ne.” To ana bayyana maka kenen cewa wannan mutumin ya fita daga duhun-kai. Ya fuskanci ainishin yanayin rayuwa da kuma yadda ya kamata ya yi mu’amula da jama’a. kamar haka ne kuma in ka ji kishiyarsa, ka tabbata wannan wani mutum ne maras kyakkyawar fahimta. Wanda kuma tabbas ba zai yi dadin mu’amula ba. Ba mamaki, shi ya sa dukkanninmu muke kwadayin yin tarayya ko mu’amula da wayayyun mutane, muke kuma tsoron fara ta da wadanda ba su waye ba.

Wayewa, tamkar ilimi take. Takan iya zama fanni-fanni. Wato dai kamar yadda mutum zai yi wani nau’in karatu har ya kai matakin malami a ciki, amma kuma ka taras da shi idan an zo wani fagen ya zama dan kallo. Haka nan akan samu mutumin da ya ke da wayewa a wani fanni na rayuwa, amma ba shi da ita a wani. Ko kuma ma ka taras mutumin da ake ayyana shi a matsayin wayayye a wani garin da zarar ya sauya gari sai ka taras ya bace a rububi. Sam ba a iya irga shi a cikin wayayyu a wannan sabon garin.

Idan mun fahimci wannan, to ya kamata kuma mu yarda cewa, a cikin zamantakewar aure ma, akwai mutanen da su ka waye, akwai kuma masu duhun kai. Kuma tamkar yadda mutumin da yake da ilimi yake jin dadin rayuwa, a karan kansa. Kuma wadanda suke mu’amula da shi suke jin dadin mu’amular, haka ne kuma wanda yake da wayewa irin ta zamantakewar aure yake more jin dadin rayuwar auren. Kuma wadanda suke mu’amular auren da shi ma suke jin dadin zaman. Yayin da a gefe guda kuma wanda ba shi da wannan wayewar yake shan wahalar zaman. Kuma wadanda suke mu’amular auren da shi sukan zama mafiya shan wahalar rayuwa irin ta aure. Ba ma wai maganar jin dadin suke yi ba su.


Idan lamarin ya tabbata haka, za mu iya cewa daga mafiya girman abubuwan da suka kamaci mutum a rayuwa, bayan ilimin sanin Allah subhanahu wa ta’ala, da yadda za a bauta maSa. To akwai kuma sanin yadda za ka samu wayewa irin ta zamantakewa. A matsayinta na bangare muhimmi daga bangarori mafiya girma a cikin rayuwar kowannenmu. Domin a cikin zamantakewar ne ake samun jin dadi da riba da nishadi irin na wannan rayuwar, ta duniya. Haka nan kuma a cikintan ne ake samun yadda mutum zai kai ga samun rahamar Ubangiji mabuwayi, a can lahira.

Daga cikin mafiya bin sha’awar lamarin da yake faruwa a cikin gidajen wayayyun ma’aurata shi ne samun farin ciki, kari a kan wanda marasa wayewar kan samu. Da kuma rage kaifi ko zafin damuwa, ragi mai girma kan wanda marasa wayewar kan samu.

Daga cikin abubuwan kallo ko labari mai ban sha’awa, akwai na irin rayuwar da take gudana a gidan wayayyun ma’aurata. Saboda yadda suke tafiyar ta mu’amuloli tsakaninsu. Musamman yadda suke tunkarar yanayi mai tsauri da kan zuwa wa ma’aurata. Mu dauki misali daga cikin abubuwan da muka sha tattaunawa a nan. Wayo game da yadda maza kan janye jiki ga matansu. Ba kuma tare da matan sun yi wani laifi ba. Da kuma yadda wani yanayi kan zo wa matan, wanda za a yi musu laifi kadan ya taso da damuwar laifika dari da suka shude. Ta burkita dukkan lissafin gidan, ko ma ta watsa kyawawan mu’amular da ke tsakaninta da mijin baki daya.

A Gidan Wayayyun Ma’aurata.


Maza ba su san yadda janye jikin da sukan yi ga matansu yake matukar cutar da matan ba. A lokaci guda kuma, matan ba su san cewa mazan ba su da ikon cire wannan al’ada daga dabi’arsu ba. Amma wayayyen namiji, wanda ya samu wayewa irin ta zamantakewar, duk lokacin da ya samu kansa cikin irin wannan yanayi, ba ya mantawa cewa , tsayawa a saurari mace abu ne mai matukar muhimmanci. Domin yana sane da cewa yanayin yana iya cutar da ita. A lokaci guda kuma ya san cewa girmama bukatunta ma abu ne mai matukar muhimmanci. Don haka yakan iya daurewa shi da kansa ya danne tasa damuwar. Ta hanyar bude fagen hirarsu da tambayar ta me ne ne yake damun ta. Sannan zai iya jurewa ya saurari bayananta tiryan-tiryan. Alabasshi daga karshe ya nemi ta ba shi lokaci ya yi nazarin maganar, in ya so sa yi mata zama na biyu, su tattauna yadda za a warware matsalar. Ba tare ma da ta fahimci son maganar ne ba ya yi a wannan lokacin ba.

Haka nan, akwai yanayi da yakan zo wa magidancin wanda ma zai ji kamar ba zai iya samun damar sauraren ta ba. A irin wannan lokacin, wayeyyen magidanci yakan iya cewa matarsa. “Ki yi hakuri, ina cikin wani yanayi da nake bukatar ji na ni kadai. Amma ba wata damuwa ba ce, zan kuma warware cikin lokaci kadan in dawo mu ci gaba da duk abin da ya kamata.” Wannan shi zai kwantar mata da hankali. Maimakon barin ta cikin zulumi da akan yi a wasu gidaje.

A hannu guda kuma, wayyayyiyar mace, ba ta bukatar wani dogon turanci a wannan fage dama. Don haka, da zarar magidanci ya yi irin wancan kalami, to ta san abin da yake faruwa. Za ta janye ta ci gaba ta nata harkokin.

Sannan wayayyiwar mace ta san dukkan wasu hanyoyi da za ta bi ta taimaki mijin yayin da yake cikin irin wannan yanayi. Ta hanyar samar masa da irin yanayin da ya fi bukata. Yanayi na shiru, wanda ko yara ba za ta bari su yawaita hayaniya a cikin gidan ba. Balle karar Talbijin da rediyo, musamman na sautukan da ba ya so. Amma idan wani abu za ta kunna ma, ta san irin wanda ya fi son ji. Don haka a lokacin ita ma shi za ta ji, ko da kuwa ba ta so. Haka nan ta san duk abin sha ko na ci da ya fi so. Za ta samar da su. Mutumin da ya samu irin wannan yanayi, to shi ne mafi saurin dawowa hayyacinsa


Haka kuma, mace wayayyiya, yayin da yanayin murdawar igiyar ruwa da yakan zo wa mata ya zo mata. Ta san yadda za ta yi, ta yi maganganunta ba tare da dora masa dukkan laifukan damuwarta a kansa, kai tsaye ba. Kenan tana cikin yanayin, amma tana kuma sane da cewa wannan yanayin fa zai wuce.

A daya hannun, namijin da yake da wayewa, zai tsaya ya saurari matarsa lokacin da wannan igiyar ruwan tata ta murda. Zai kuma bar ta ta yi fadanta da lissafin damuwarta ta gama, ba tare da ya tanka mata ta yadda za su kara dagula lamarin ba, domin ya na sane da cewa wannan wani yanayi ne da zai zo ya gushe na dan wani lokaci.

Har wayau, yana da masaniyar yadda zai bi ya nuna mata soyayya da kulawa, yadda cikin kankanen lokaci ita da kanta za ta fara karyata kanta. Musamman game da maganganun da ta yin a zargin ba a damu da ita ba. Yayin kuwa da gida ya zama haka, ai alhamdulillahi! 


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top