*Akwai mazan da za su iya dabawa da kafarsu zuwa Legas, idan har hakan ne sharadin da na basu na aurena."

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Shahararriyar 'yan wasan fim din Hausa, Rukayya Dawayya, ta bayyana cewa har yanzu tana jin ciwon yadda tsohon mijinta, Adamu Teku, ya sake ta ta hanyar sakon tes din wayar salula.

Dawayya ta bayyana hakan yayin wata tattaunawa da wakilin jaridar Blueprint, Aliyu Askira.

Da take amsa tambaya a kan shin tana nadamar auren Adamu Teku, kasancewar tun kafin ta aure shi an gargade ta a kan kul ta aure shi saboda ya yi soyayya da 'yan matan masana'antar fim din Hausa masu yawa kuma da kyar ya shafe watanni shida da mace bai rabu da ita ba, Dawayya sai ta ce: "A matsayina na Musulma, nadama ba ita ce amsar da ta kamata ba. Amma maganar gaskiya, har yanzu ina jin ciwon yadda tsohon mijina ya yanke shawarar rabuwa da ni ta hanyar test din wayar hannu.

"Wata rana babata ta zo daga Saudiyya, sai na nemi izinin mijina kan in je Kano domin in gan ta. Shi kuma bai ki ba, ya ba ni izinin in je.

"Na tashi sai Kano tare da dana Arafat. Da na isa Kano nai ta kiran shi amma ya ki daga kiran ko kuma ya amsa sakonnina na tes din waya. Abin da na gani daga karshe shi ne sakon tes da ya turo min kan ya sake ni saki uku, ma'ana ba zan koma ba har sai na auri wani mutum daban.

"A matsayina na 'ya mace, wannan wani abu ne mai matukar ciwo a rayuwata. Ban cancanci haka ba saboda ina da matukar kyau, kuma zan iya daukar hankalin duk wani da namiji. 

"Da na auri Adamu Teku, na gano abubuwa da yawa game da shi wadanda na yanke shawawar jurewa saboda ina so aurena ya dore." 

Da aka tambaye ta a kan wadanne abubuwa ne ta gano a game da shi bayan ta aure shi sai ta ce, "Dan uwa, ba za ka amince da jin cewa na gano cewar kafin ni, Adamu Teku ya auri mataye 24. Ya haifi yara da yawa da mataye daban-daban. A gaskiyance, yana da 'ya'ya tara kuma kowanne babarsa daban. Yana kuma da 'ya'ya manya, ciki har da 'ya mace wadda ta zama kawata. Ita ta zamo wadda ke lallashi na. A lokuta da dama ita ce wadda ta dinga ba ni shawara kan in yi hakuri in zauna. 

"Kamar yadda na fada a baya, kafin in yi aure ina samun rufin asiri a  kasuwanci. Na zuba jari a kasuwanci da yawa a Kano. Don haka, bayan na fara fuskantar matsaloli a gidan auren, ban taba jira mijina ya aje min abinci ba, saboda na ci burin sanya aurena ya dorewa. Amma duk da haka, da na tafi Kano domin gano babata wadda ta dawo daga Saudiyya, sai tsohon mijina ya yanke shawarar aika min sakon tes, yake ce min aurenmu ya zo karshe. Kuma shi ne wanda muke kira saki uku saboda kirikiri ya bayyana cewa zan iya yin aure idan na gamu da wani wanda yake so na. Tun daga nan na ci gaba da fafiyar da rayuwata, kuma ina farin cikin ina da da, Arafat, wanda yake na sunna, kuma kasuwancina yana tafiya yadda ya kamata.

"Saboda haka, ina cikin lafiya da kwanciyar hankali. A gaskiya, akwai mazan da za su iya dabawa zuwa Legas, idan har hakan ne sharadin da na basu na aurena."

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top