Hausawa na kiranta KUBEWA, Turawa na cewa LADY’S FINGER  Amerikawa na ce GUMBO mutanen Spain na ce mata  GUIBEIRO yayinda a India ake ce mata  BENDAKAI. Amma dai duk an yi imanin cewar KUBEWA ta samo asali ne daga kasar Habasha wato Ethiopia da kuma Masar wato Egypt tun karni na 12. Mutane da dama na ci ko sham miyar kubewa saboda dadinta ne kawai amma ga kadan daga cikin  amfaninta a matsayin magani wanda aka shafe shekaru dauruwa ana amfani da ita.A wasu kasashen Turai ma har packaging ake mata a matsayin magani.

1. Ana amfani da kubewa wajen maganin  ciwon sugar wato  Diabetes. Saboda abinda ake kira (fiber ) a cikinta, na amfani wajen daidaita yawan suga a cikin  jiki, wanda kuma ke rage karfi ciwon sugar ko ma maganinsa.
2. Masu ciki kan iya amfani da kubewa domin ingancin lafiyarsu da kuma na jaririn da ke ciki domin kubewa na kunshe da  dimbin Vitamin B da ke samarwa da kuma inganta sabbin kwayoyin halitta na gina jiki (cells) da kuma ( folates) don haka kubewa na hana haihuwar jariri mai dauke da wasu nakasu a jikinsa  kuma na sa jaririn ya  girma a ciki kuma da koshin lafiya yadda ake so. Haka kuma jaririn da ke ciki  zai iya amfana da dimbin Vitamin C dake cikin kubewa domin kare lafiyarsa.

3. Kubewa na maganin ciwon koda. Wani bincike  daga jami’ar Jilin ta kasar Sin ya tabbatar da  wannan. Binciken. Ya nuna cewar wadanda suke ci ko shan kubewa a kullun  sun nuna nasarar rashin lalacewar koda  musamman wadanda ke da ciwon sugar domin kusan kasha 50 na masu matsalar koda sun samu matsalar ne saboda suna da ciwon sugar.
4. Kubewa na kara lafiyar dubura (colon)  wato karshen babban hanji.yana wanke hanji da tumbi sosai don haka yana maganin kumburin ciki. Kuma Vitamin A da ke cikin kubewa na taimakawa lafiyar  wani abu kamar majina  ( Mucous membranes) na cikin babban hanji.

5. Kubewa na  maganin Asthma da wasu cututtukan numfashi. Yana dauke da Vitamin C da ke taimakawa hanyoyin numfashi.
6. Kubewa na kara ingancin fatan jikin mutum yay i laushi da santsi kamar yaukin kubewa. Ka ga mutum kullun kamar yaro ko yarinya a fatarsa.Yana  kuma taimakawa wajen mayar da fatar da ta lalace.
7. Yana  matukar maganin Anaemia wato karancin jini a jiki domin kubewa na kunshe da sinadarin Iron sosai. Kuma yawan amfaani da kubewa na sanya idan ka ji rauni jini ba zai zuba da yawa har yay i maka lahani ba. (blood coagulation)

8. Yawan sha ko cin kubewa na matukar rage nauyin jiki  ga wadanda suke jin kiba ya musu yawa.
9. Wani sinadari a cikin kubewa da ake kira  (soluble fibre) yana taimakawa wajen rage cholesterol wanda kuma hakan ke rage yiyuwar kamuwa da ciwon zuciya sannan na taimakawa wajen samar da ingantaccen ruwan data (madaci) a hanji
10. Amfani da kubewa a kai a kai na inganta kashin mace da namiji  kuma na maganin dandruff. Za ka tafasa ruwa tare dayankakken danyen kubewa, idan yay i sanyi sai ka matse rabin lemon tsami a ciki sai ki rinka wanke kanki ko kanka da ruwan. Kuma yana kasha kwarkwata ma.

11. Kubewa na kara kare lafiyar garkuwan jiki ya kuma rage maka yawan kamuwa da cututtuka. Sinadaran Vitamin ce da calcium da magnesium da sauransu da ke cikin kubewa sukan taimaka wajen yaki da abubuwa marasa kyau a jikin mutum.
12. Kubewa na kara ingancin lafiyar ido da kuma hana kamuwa da yanar ido domin yana kunshe da Vitamin A da carotene masu yawa a cikinsa. Mai yawan shan kubewa zai iya tsufa da idanunsa garau.

YANDA AKE AMFANI DA SHI.
RUWAN KUBEWA.
A sa kubewa guda biyu zuwa uku (gudansa) a ruwa maras zafi ko dumi a cikin kwano ko gilashi a barshi ya kwana , sai a cire kubewar da safe a shanye ruwan. Kullun a rinka yin haka har kwanaki talatin ko fiye domin samun sakamakoo mai kyau. Ana iya cigaba da hakan.
Ko mua a yankan kubewar  a sanya cikin ruwa a barta ta kwana sannan a shanye ruwan kullun da safe. Amma za a dan ji daci daci.
Sannan  ana iya mafani da wuka a fere kubewar wato bawonsa mai aunin kore sai a ci bawon kai tsaye danyensa amma kar ya wuce rabin cokalin shan shayi a lokaci guda.
Ko kuma  a cire yayan kubewar a sanya su bushe sannan a nika har su zama gari  sai a rinka sha da ruwa. Amma kada a sha ya
wuce 5gm a rana.
Ana kuma yin tea da ganyen kubewa. (sources: information,com and pinterest.com)
LALLAI NE KA TUNTUBI LIKITANKA KAFIN SOMA AIKI DA KOWANE IRIN MAGANI!
Allah sa mu dace.



©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top