A zaben gwamnan jihar dai da aka gudanar, Abba Kabir Yusuf wanda ake ma inkiya da Abba gida-gida ya sha kashi a hannun Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, duk da cewar shine ke a kan gaba a zaben farko wanda hukumar INEC ta bayyana a matsayin ba kammalalle ba.
Sai dai masu sa ido na gida da waje sun soki tsarin gudanarwra karashen zaben inda suka yi zargin cewa an tafka magudi, zargin da jam'iyyar APC da kuma hukumar zabe suka karyata.
Kotun dai tana da kwana 180 ne ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar. A ranar 11 ga watan Afrilun 2019 ne Abba ya shigar da karar.
Ke nan kwanaki 97 ya rage ita wannan kotu ta kammala shari'ar domin yanke hukunci.
Zaman kotun na ranar Alhamis wanda mai shari'a Halima Shamaki ke jagoranta, ya mayar da hankali ne kan tantance bayanai da korafe-korafen da bangaren masu kara da na masu kare kai suka gabatar.
An dai tabka muhawara a tsakanin lauyoyin, inda kowane bangare ya nemi da a kori karar da daya bangaren ya shigar kafin daga bisani kotu ta cimma matsayar dage zaman.
Lauyoyin da ke kare Ganduje sun bukaci da a dage sauraron karar, tare da ba su isasshen lokaci domin yin nazarin wata sabuwar bukatar da masu kara suka gabatar.
Su ma masu gabatar da karar sun ki amincewa da ita, sakamakon zargin da suke yi cewa lauyoyin da ke kariya na fitar da salo ne kawai na ba ta lokaci.
Dan takarar gwamna na jam`iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf da kuma jam`iyyarsa ne suka shigar da karar bisa zargin cewa zaben cike yake da magudi da kuma aika-aikar `yan bangar siyasa.
Haka kuma masu karar sun bukaci kotu ta yi watsi da sakamakon zaben da aka yi, zagaye na biyu, wanda aka fi sani da "Inconclusive," bisa zargin cewa babu tsarin Inconclusive a cikin dokar zabe.
Abba da kuma jam`iyyarsa na karar Hukumar Zabe ta Kasa, INEC da Gwamna Ganduje ne, amma sun musanta zarge-zargen na PDP.
Yanzu dai kotun ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 13 ga wannan watan na Yuli, don ci gaba da shari'ar.
©HausaLoaded
Post a Comment