*
2-Bleaching da mata suke yi yana zama daya daga cikin silar rashin samun mijin Aure!!!
*
'Yar Uwata duk wanda yace miki gaba daya Maza fararen Mata suke so, Qarya yake yi.
*
Daga cikin Maza akwai masu son fararen Mata, Sannan akwai masu son Baqaqen Mata, ba ko wanne Namiji bane yake son Farar Mace.
*
Na san wanda aka saka ranar Auren sa, da wata Budurwa ya biya Sadakin ta ya gama komai rana yake jira, a satin da za'a daura musu Aure ya dawo daga inda yake harkokin sa, domin bukin, yace ya fasa Auren ta, saboda tayi Bleaching tayi fari, shi kuma lokacinda ya ganta baqa ce, kafin ya dawo ta koma fara ta canja daga asalin yadda ya santa, yace ya fasa Aurenta a bashi kudinsa ya nemi wata, shi Farar mace ba ra'ayinsa bace, ballantana farin Bleaching, Auren da aka fasa kenan, har yanxu yarinyar tana nan bata Auru ba!
*
'Yar Uwata idan kika yi Bleaching kika canja fatar ki ta asali, daga Baqa kika koma Fara, idan Namijin da yake son Farar mace ya Aure ki cikin rashin sani, bayan kunyi Aure haqiqanin fatar ki ta fara bayyana, ta yadda zai gane cewa kin sayi farin ne da kudin ki, zai daina sonki idan yaga kin fara koɗewa, wulaqanci zaki sha, daga bisani zai rabu dake.
*
Qawarki wacce ta amince da halittar ta, bata canja ta koma fara ba, Allah zai kawo mata Mijin da yake son Baqa, ya Aureta su zauna cikin Aminci da mutuntawa, kullum soyayyarta qara qaruwa zata dinga yi, a cikin zuciyarsa saboda ya Auri zaɓin sa!
*
A cikin Matan Tsofaffin Shugabannin Qasar mu, Nigeria da mataimakan su, da masu ci yanxu, Akwai masu Auren Mata Farare, da kuma masu Auren Mata Baqaqe.
.
Daga cikin Matan Gomnonin Nigeria masu ci yanxu, da tsofaffin Gomnoni, akwai Masu Auren Baqaqen Mata da akwai masu Auren Fararen Mata.
.
Haka abin yake a cikin Ministoci, 'Yan Majalisun Tarayya da kuma na Jihohi, da Duk wani ɓangare na matsayin Mutane. 
.
Duk wacce take son ta zauna cikin gidan mijinta kullum soyayyarta ta dinga qaruwa a cikin zuciyarsa, to, ta yarda da halittar da Allah yai mata, Allah zai kawo mata wanda yake kallon 'Yan Matan duniya da siffar Maza, Ita kaɗai yake gani da siffar Mata.
.
'Yar Uwata ba Macen da Mijinta yake rabuwa da ita saboda Baqa ce, Amma ana sakin Mace idan ta fara koɗewa, alamu suka nuna cewa asalinta baqa ce!
.
'Yar Uwata, duk da, ce muku da ake yi, Maza Fararen Mata suke so, ya akayi Baqaqen ake samun masu Auren su?.
.
(FARAR MACE LANTARKIN GIDA)
(BAQAR MACE AL-JANNAR MAZA)
.
Yaa Allah ka baiwa Maza, Mata Masu Addini da Kyawawan Ɗabi'u Ameen.
Yaa Allah ka baiwa Mata, Mazan Aure Nagari Ma'abota Addini masu Kyawawan Ɗabi'u Ameen.

Mal. Fakihu M. Sani Jingir


© Sirrinrikemiji

Post a Comment

 
Top