"Na fara zuwa sai na ga abu ne da ake yi kullum, sai na koma ina ba da shawara kan matakan da ya kamata a dauka," a cewar Yarima, wanda ke magana a karon farko da wata kafar yada labarai tun bayan da jam'iyyarsa ta APC ta rasa mulkin jihar.
A cikin hirar, wacce ya tatattauna batutuwan da suka shafi tsaro da siyasa da kuma shari'a, ya fadawa Awwal Janyau cewa zuwansa jaje ba zai kawo karshen matsalar tsaro a jihar ba.
Jihar Zamfara na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya inda ake yawan samun kashe-kashe da sace-sacen mutane, lamarin da ke jefa mazauna yankin cikin fargaba da raba wasu da gidajensu.
Wasu 'yan Najeriya, musamman ma a jihar, sun dade suna alakanta matsalolin da rashin samun shugabanci nagari tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya.
Kuma Sanata Yarima, wanda shi da abokan siyasarsa suka shafe shekara 20 suna mulkar jihar, ya amince cewa talauci ne ya jefa jihar cikin halin da take ciki a yanzu.
Shari'a
Sanata Yariman Bakura ne ya fara kaddamar da Shari'ar Musulunci a Najeriya, inda daga baya wasu jihohi suka yi kokarin kaddamar da tsarin na Shari'a.
Sai dai tun zamanin mulkin shari'a a Zamfara ake fuskantar rikicin makiyaya da manoma, da satar shanu wadanda ake ganain su ne suka ta'azzara suka koma fashi da makami da satar mutane a yankin arewa maso yammacin kasar.
©HausaLoaded
Post a Comment
Click to see the code!
To insert emoticon you must added at least one space before the code.