Ana iya yada kwayar HPV a yayin kowane irin lamari da ya shafi saduwa, wadda ita ce take jawo mafi yawan sankarar mahaifa.
Amma wani bincike ya nuna cewa daya daga cikin mata biyar 'yan madigo ba sa zuwa gwaji.
Masana lafiya sun ce ya kamata duk wadda take da mahaifa kuma tana tsakanin shekaru 25 zuwa 64 ta dinga zuwa gwaji akai-akai.
An samu adadin ne daga wani rahoto na dabi'ar 'yan madigo wajen yin gwajin mahaifa a Kudu maso Yammacin Ingila.
Yayin da da yawan mata ke bukatar zuwa gwajin sankarar mahaifa, kashi 8 cikin 100 na 'yan madigo ba su taba zuwa ba, ko ma ba su san muhimmancin hakan a gare su ba.
Kashi 21 cikin 100 kuma na tunanin mata 'yan madigo ba sa fuskantar barazanar kamuwa da kansar mahaifa idan aka kwatanta da masu bin maza da kuma yin madigon a lokacin guda.
An yi binciken ne a kan fiye da mata 600.
NHS ta Ingila ta ce hakan na nufin fiye da 'yan madigo 50,000 ba su taba yin gwajin mahaifa ba.
Dokta Michael Brady jami'i a hukumar NHS kuma mai bai wa kungiyar 'yan luwadi da madigo LGBT shawara, ya ce:
"Camfin da ake yadawa cewa 'yan madigo ba sa fuskantar barazanar kamuwa da sankarar mahaifa ba haka ba ne, domin hakan ya jawo dubban mutane da dama ba sa zuwa gwaji, kuma hakan abin damuwa ne ga al'ummarmu.
"Ya kamata mu gane cewa kansa ba ruwanta da wariya, tana iya kama kowa.
"Idan dai har kina da mahaifa to za ki iya kamuwa da sankarar mahaifa, kuma ana iya yin riga-kafinta, ya kamata mutane su dinga yin gwaji akai-akai."
'Camfe-camfe masu cutarwa'
An yi wa fiye da kashi 71 cikin 100 na mata da ke tsakanin shekaru 25 zuwa 64 gwaji akai-akai, kamar yadda alkaluman shekarar da ta gabata suka nuna.
Gwajin sankarar mahaifa da ake kira Pap Smear, na taimakawa wajen gano cutar tun tana matakin farko-farko.
Wata kwayar cuta da ake kira Human Papillomavirus (HPV) ce take jawo kusan dukkan sankarar mahaifa.
Farfesa Anne Mackie, daraktra a cibiyar gwaji ta Ingila, ta ce matan da ke madigo za su iya kamuwa da kwayar cutar HPV a yayin saduwa.
"Don haka dole ne mu karfafawa duk wadda ke da mahaifa gwiwa da ke tsakanin shekara 25 zuwa 64, su dinga yin gwaji akai-akai."
Robert Music na kungiyar Jo's Cervical Cancer Trust, ya ce: "Dole ne a yi gaggawar kawar da camfe-camfen da ake yadawa cewa gwajin sankarar mahaifa ga 'yan madigo ba shi da muhimmanci.
"Gwajin mahaifa zai kasance mai wahala saboda dalilai da dama kuma dole mu mayar da hankali wajen kawar da shingen ke tsakani mu kuma tabbatar da cewa kowane mutum mai hankali ya fahimci amfanin gwajin sankarar mahaifa."
Hukumar NHS ta Ingila za ta samar da wata sabuwar hanya ta gwajin mahaifa nan da shekarar 2020.
@bbchausa
©HausaLoaded
Post a Comment