An sanar da sunan Nicki Minaj a matsayin wadda za ta gabatar da wasa a dandalin wani taron raye-raye na shekara-shekara a Saudiyya, abin da ya jawo hayaniya a ciki da wajen kasar game da yadda abin zai kasance a kasa mai "tsauri" irin Saudiyya.

Mawakiyar hip pop din ta Amurka za ta gabatar da wasan ne a bikin Jeddah World Festival ranar 18 ga watan Yuli da muke ciki.

Wasan da za ta yi yana daya daga cikin irin sauye-sauyen da Saudiyya ke samarwa game da harkar nishadantsarwa a kokarinta na habaka bangaren adabi a kasar.

Sunan "Nicki Minaj" yana cikin kalmomin da suka yi fice a shafin Twitter a ranar Laraba yayin da mutane ke ta bayyana ra'ayoyinsu game da sanarwar.

Wani mai amfani da shafin ya ce: "A ce kawai yanzu kana farkawa daga dogon suma a fada ma cewa Nicki Minaj za ta yi wasa a Saudiyya, ai zan zaci cewa a wata duniyar daban na farka."

Shi kuwa wannan tambaya yake kan ko an nemi karin bayani a kan Nicki Minaj a Google kafin a gayyato ta:

Ra'ayoyin ba duka ne masu sauki ba da kuma goyon bayan abin. Wani ya ce sam abin bai dace ba in aka kalli kusancin garin Jeddah da Makkah gari mafi tsarki a duniya.

Ita kuwa wata mata bidiyo ta wallafa a shafinta, inda take korafin cewa ta yaya za a gayyato Nicki Minaj Saudiyya kuma a tilasta masu saka doguwar abaya.

"Za ta zo ta yi murgude-murgude kuma ta yi wakoki kan jima'i da fitsara amma kuma ku ce min na saka abaya. Shirme kenan?"

Wasu kuwa sun bayyana cewa zuwanta kasar yunkuri ne kawai na yada madigo ganin yadda kasar take da tsauri kan 'yan luwadi da madigo - hukuncin kisa ne ake yanke wa 'yan luwadi da madigo a Saudiyya.
Minaj ba ita ce ta farko ba da ta haddasa ce-ce-ku-ce a kan amsa gayyatar yin wasa a kasar. Mawakiya Mariah Carey ma ta gabatar da nata wasan duk da irin kiraye-kirayen da masu fafutikar kare hakki suka yi mata da kar ta yi.

Mawaki Nelly ma ya sha suka sosai bayan ya gabatar da wasan maza zalla a kasar.

Wannan sassauci kan harkokin nishadantarwa na baya-bayan nan da Saudiyya ke yi wani bangare ne na shirin da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake yi na fadada harkokin tattalin arzikin kasar.

Turki Al al-Sheikh shi ne shugaban hukumar nishsadantarwa ta kasar kuma tun a watan Janairu ya shimfida hanyar ciyar da bangaren gaba a wani sako da ya wallafa a Twitter.

"Da yardar Allah alkiblar harkar nishadi a shekaru masu zuwa za ta kasance ta hanyar hada tarukan wasanni na dandali da wuraren shakatawa da wasannin kwaikwayo domin ci gaban matasa da kuma tallafa wa kamfunnan nishadantarwa na kasa."

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top