Gyaran jiki ta hanyar yin alawa abu ne da yake raba fata da duk wani gashi da daudar da ta makale ko kananan kuraje a fatar mace.
Duk da cewa akwai hanyoyi da dama na kawar da gashi a jikin mutum, amma kawar da gashi ta hanyar alawa ta fi sauri da inganci, domin ita ba cire gashin kawai take yi ba, tana ma kara wa fatar laushi da walkiya. Duk da cewa yin alawa na da dan zafi a kan fata, matan da suka san darajar kwalliya a kullum a shirye suke su gyara jikinsu ta wannan hanya.
Haka kuma wannan hanya ita ce mafi sauki kasancewar aba ce da ba ta bukatar kashe wasu makudan kudi. Abin da kawai kike bukata shi ne ruwa da sukari da lemon tsami. Za ki hada wadannan kayayyaki a tukunya sai ki dora a wuta, amma ki daidaita wuta yadda ba za su kone ba. Sai ki bar su su yi ta dahuwa har sai sukarin ya narke.
Idan hadin ya zama ruwan kasa sai ki sauke ki bar shi ya huce. Idan ya huce sai ki gwada yanayin zafinsa ta hanyar zuba shi a hannu. Idan ba zafi sosai sai ki ci gaba a sauran wuraren jikinki.
Ga yadda ake yin alawar:
Za ki fara da wanke wurin da kike son yi wa alawar, idan kika tabbatar ya bushe sai ki rika debo ruwan sukarin, kina zubawa a kan fatarki, wato a wurin da kike son yi wa alawar.
Kada ki zuba shi da yawa a wuri daya. Ba a son ya yi kauri a kan fata, domin hakan zai sa abin ya yi zafi zau a kan fata. Haka kuma ba zai yi aikin da ake bukata ba.
Daga nan sai ki yi kokarin cire shi a hankali har ki daye shi daga kan fatarki. Idan kika gama cire shi sai ki yi wa wurin dilke, wato irin goge fatar nan da ake yi da kayan hadin dilke. (Za mu kawo bayani sosai a kan dilke wani lokacin).
Kasancewar alawa tana fitar da duk wani gashi, hakan kan sa fata ta yi sumul da taushi, ta yadda za ki iya yin takara da jinjiri.
Haka kuma, takan sa fatar jiki ta yi santsi da walkiya da kuma haske. Ana kuma son a rika yin wannan alawa bayan duk mako hudu zuwa shida.
© Sirrinrikemiji
Post a Comment