Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta jajirce wajen rage babbar tazara dake tsakanin Talakawa da kuma attajirai yayin neman ta akan shimfida dokar ta baci musamman a fannin sarkakiya ta rashin aiki a fadin kasar nan.

Majalisar ta kuma nemi gwamnatin tarayya da ta habaka tanadin kasafin kudi domin inganta harkokin ilimi da hakan zai taimaka kwarai da aniya wajen kawo karshen lalaci a tsakanin matasa da kuma rashin tsaro a fadin Najeriya.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, a cewar majalisar tarayyar Najeriya, ci gaba da ta'azzarar miyagun ababe masu haifar da rashin tsaro a fadin kasar nan na da babbar nasaba da halin ko-in-kula da attajirai ke yiwa talakawa.

Bisa ga kudirin dan majalisa mai wakilcin shiyyar Enugu ta Arewa a karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Chukwuka Utazi, majalisar yayin zaman da ta gudanar a ranar Larabar da ta gabata ta tattauna batutuwa akan barazanar da kasar nan za ta fuskanta a sakamakon halin ni'ya su da talakawa ke ciki.


Cikin neman warware wannan muguwar annoba da za ta jefa kasar nan cikin tsaka mai wuya, majalisar ta gargadi shugaba Buhari akan inganta jin dadin rayuwar talakawa, da hakan zai kawo sauki na tashin-tashinar bore da suka fara wajen aikata ta'addanci akan masu hannu da shuni.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top