Sabon sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, a ranar Laraba, 15 ga watan Mayu ya bayar dalilinsa na karban nadin nasa
- Sarkin yace ya amshi shugabanccin Bichi ne saboda ya san cewa lokaci zai sauya abubuwa
- Bayero ya kuma ce Muhammadu Sanusi, Sarkin Kano dan uwansa ne kuma ba zai yi fushi da nadinsa ba
Sabon Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, a ranar Laraba, 15 ga watan Mayu yayi bayani akan dalilinsa na amsar nadin da aka yi masa domin ya zama Sarki.

Yayinda yake jawabi a manema labarai a wani taron manema labarai, Bayero yace ya amshi tayin zama sarkin Bichi ne saboda lokaci na sauya abubuwa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sabon sarkin yace daga 1963 lokacin da mahaifinsa a zama sarkin Kano har zuwa yanzu, sauye-sauye da dama su afku kuma lokaci zai ci gaba da sauya abubuwa.



Yace: "Bari na baku misali da kaina. Marigayi mahaifina ya nada ni Danmajen Kano a 1990; daga bisani na zama Danbura Kano, sannan na zama Turakin Kano zuwa Sarkin Dawakin Tsakar FGida sannan daga karshe na zama Wamban Kano.Na san zai baku mamaki idan nace Wallahi ban taba zuwa wajen wani ina neman ko daya daga cikin nade-naden nan ba.
"Don haka a wajena kafa sabbin masarautu ba komai bane face sauyi dake zuwa daga lokaci zuwa lokaci. a wajena, samun sarakuna biyar a Kano ba zai shafi ci gaban jihar ba idan har sarakunan za su iya aiki tare cikin zaman lafiya da amana.

"Idan har sarakunan sun damu da ci gaban Kano, za su iya aiki tare sannan su kawo ci gaba a jihar. Babu wani banbanci a tsakaninmu duka."
Bayero ya kuma yi magana akan alakarsa da sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, cewa suna da mutunta juna sannan kuma nadinsa ba zai fusata shi ba.

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top