Suna: Rana Bata Karya
Tsara Labari: A. U Usman
Kamsni: Alhayat International
Shiryawa: Hayatuddin Yakubu
Umarni: Husaini Ali Muhammad
Jarumai: Adam A. Zango, Baballe Hayatu, Isa A. Isa, Shu’aibu Lawan, Umar Gombe, Ibrahim Mandawari, Hajara Usman, Rukayya Dawayya, Fiddausi Muhammad. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Lamir (Adam A. Zango) a zaune cikin ofishin sa yana waya da budurwarsa wadda yake son aura, yayin da daga bisani kuma Sani (Baballe Hayatu) abokin aikin sa ya shigo office din ya kawo masa wasu takardun fili har yake zolayar Lamir akan soyayyar sa da budurwar sa Munibiya.
Munibiya (Fiddausi Muhammad) ta kasance kyakykyawan mace wadda samari suke rububi wajen son ganin auren ta, sai dai kuma tana da halin yaudara domin duk saurayin da suka hadu takan nuna masa cewar shi ne kadai take soyayya dashi kuma wanda zata aura, hakan yasa samarin ta gaba daya suka yarda da cewar so na hakika take yi musu. Amma a zuciyar Munibiya ta zabi Lamir (Adam A. Zango) a matsayin mijin da zata aura, sauran manema auren ta kuma ko wanne da akwai dalilin ta na yin tarayya dashi.
Akwai lokuta daban daban wanda Munibiya idan sun fita yawon shakatawa da saurayin ta Lamir wasu samarin suke nuna sun san ta kuma suna soyayya da ita, amma sai ta nuna ita bata san su ba. Tun abin baya damun Lamir har wasu wasi da zargin budurwar tasa ya soma shiga zuciyar sa, amma sai abokin aikin sa Sani ya nuna masa illar zargi wanda hakan yasa Lamir ya watsar da tunanin komai har zuwa ranar daurin auren sa da Munibiya, wanda a ranar ne ya fito ya nuna bazai iya auren ta ba. Ganin an fasa auren ne hakan ya tashi hankalin iyayen sa da na Munibiya wadanda suka ci alwashin kai karar Lamir gaban kotu don son sanin dalilin da yasa ya tozar ta su.

A sannan ne iyayen sa suka saka shi a gaba suka je gidan iyayen Munibiya don ya fadi abinda yasa ya fasa auren ta, zuwan nasu kuma yayi daidai da likitan da ya duba lafiyar Munibiya sa’in da bata da lafiya, anan ya kawo sakamakon cewa tana dauke da juna biyu, anan ne shima Lamir ya fadi lokacin da yaga shigar ta hotel tare da saurayin ta ATM (Shu’aibu Lawan)
Bayan iyayen Munibiya sun tuhumeta yadda akayi ta samu juna biyu anan ta bada labarin yaudarar da ta yiwa samari mabanbanta wanda a cikin su bayan daya ya gane yaudarar sa tayi, hakan yasa ya kaita hotel da zummar sun je ziyara har yayi mata fyade, dalilin hakan ne kuma ta samu juna biyu. Jin hakan yasa iyayen ta suka yi wadarai da halin ta yayin da itama Munubiya tayi nadamar halayyar ta ta yaudara wanda ya zamo silar zubewar mutuncin ta.

Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, kuma har fim din ya kare labarin bai karye ba.
2- Hoto ya fita radau, haka ma sauti ba laifi.
3- Daraktan yayi kokarin ganin cewar labarin ya tafi yadda ya dace ba tare da ya karye ba, haka kuma yayi kokari wajen ganin jaruman sun yi rawar gani, domin sun taka rawar da ta dace.
4- An samar da wuraren da suka dace da labarin.
5- Wakokin fim din sun nishadantar kuma an saka su a gurbin da ya dace.
Kurakurai:
1- Lokacin da Munubiya take murnar zuwan ranar auren ta a cikin daki a gaban kawayen ta, sa’in da kawarta take ce mata kada ta fita don zuwa yin hoto da angwaye har sai an neme ta, abin daukar sauti ya fito wato ‘boom mic’. Har ila yau abin daukar sauti ya sake fitowa a karshen fim din a cikin lemar da samarin Munubiya suka rutsata don nuna mata cewar sun gane halinta na yaudara.
2- Ranar auren Lamir an nuna mahaifiyar sa (Hajara Usman) tana yi masa fada akan bai isa yayi musu karanta a ranar auren sa yazo da wannan maganar ba, sai gashi kuma a nunowa ta gaba ta fito daga daki tana tambayar sa abinda ke faruwa wanda yasa bai tafi wajen daurin auren ba, ya dace nunowa ta biyu ta zamo itace nunowar da aka fara yi tana tambayar sa dalilin zaman sa, kafin sa’in da aka nuna tana yi masa fada, domin fadan nata yana nuni da cewar ya riga ya sanar mata da kudirin sa na fasa auren Munubiya.
3- A wajen cin abinci lokacin da Sani yake bawa Lamir shawarar cewa yaje ya samu iyayen shi don sanar musu dalilin shi na fasa auren Munubiya, me kallo yaji sautin hayaniyar jama’a tana tashi sama-sama sa’ilin da Sani ke magana, ya dace a kawar da duk wata hayaniya wadda bata da alaka da muhallin da suke zaune.
4- Lokacin da Munubiya take tare da saurayin ta ATM (Shu’aibu Lawan) a wajen cin abinci, sa’in da ba’a kawo musu ruwa ko lemo ba, wanda sanadin hakan yasa Munubiya ta tashi taje karbo musu lemon tabar wayar ta a gaban saurayin nata, a sannan ne kira yayi ta shigowa wayar ta na sunan ‘Driber da sunan Recharge Card’ yayin da shima yaga tayi sabing lambar sa da ‘ATM’ amma kuma lokacin da Munubiya ta dawo daga wajen karbo lemon sai me kallo yaga ta dawo haka ba tare da komai a hannun ta ba, tamkar dama ta tafi ne don ta bawa saurayin ta damar ganin sunayen samarin da ta ajiye a wayar ta, ya dace aga Munubiya ta dawo wajen rike da abin sha ko kuma ta fadi dalilin da yasa bata karbo ba.
5- An samu ‘Discontinuity’ a wuraren da ake nuna wayar hannun Munibiya. Domin an nuna cewar tana amfani da wayar ‘handsets’ me launin Ja. Kamar irin wajen da saurayin ta ATM ya duba wayar ta a wajen cin abinci yaga sunayen samarin ta har ma da nashi da ta saka a matsayin ATM, amma a wasu wuraren kuma me kallo yakan ga Munubiya rike da waya me launin ruwan kasa kamar wajen da aka nuno ta a hotel da waya launin ruwan kasa a madadin me launin ja. Shin wayoyin Munubiya guda biyu ne? Idan har guda biyu ne ai ko sau daya ba’a taba nuna ta da wayoyin a hade guri guda ba sai dai daban daban.

Karkarewa:
Labarin ya fadakar kuma yazo da wani darasi wanda al’umma zasu amfana, domin an tabo wani bangare na matsalolin da ake samu a wannan zamanin, musamman akan ‘yan mata masu tara samari saboda kwadayi ko don son cin ma wata manufa tasu ta daban, wanda a karshe zasuyi biyu babu su dawo suna nadamar abinda suka aikata. Wallahu a’alamu!

©HausaLoaded

Post a Comment

 
Top